COVID-19: Darakta janar din NGF tare da iyalansa sun killace kansu

COVID-19: Darakta janar din NGF tare da iyalansa sun killace kansu

- Darakta Janar din kungiyar gwamnonin Najeriya, Asishana Okauru, a ranar Laraba ya ce ya killace kansa tare da matarsa Ifueko da sauran iyalansa

- Okauru ya ce yana daukar matakan ne saboda ya hadu da Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, wanda aka gano yana dauke da muguwar cutar

- Matar Okauru, Ifueko Omagui Okauru, ta taba zama shugabar hukumar kudin shiga ta tarayya kuma ita ce ta kirkiro gidauniyar DAGOMO, wacce ke tallafawa jama'a masu yawan shekaru

Darakta Janar din kungiyar gwamnonin Najeriya, Asishana Okauru, a ranar Laraba ya ce ya killace kansa tare da matarsa Ifueko da sauran iyalansa.

A wata takardar da ya tura wa jaridar Premium Times ta yanar gizo, Okauru ya ce yana daukar matakan ne saboda ya hadu da Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, wanda aka gano yana dauke da muguwar cutar.

"Na halarci taruka da dama wadanda suka hada da na gwamonin Najeriya da kuma na kungiyar tattalin arziki ta Najeriya a makon da ya gabata, wanda Gwamnan Bauchi ya halarta," Okauru yace.

"Daga nan kuma ni da matata zamu je ayi mana gwajin cutar COVID-19 a makon nan. Duk kungiyoyin da matata ke kula dasu sun komai aiki daga gida kamar yadda gwamnati ta bada umarni." yace.

COVID-19: Darakta janar din NGF tare da iyalansa sun killace kansu
COVID-19: Darakta janar din NGF tare da iyalansa sun killace kansu
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Osinbajo ya killace kansa bayan ya zauna kusa da Kyari a FEC

Matar Okauru, Ifueko Omagui Okauru, ta taba zama shugabar hukumar kudin shiga ta tarayya kuma ita ce ta kirkiro gidauniyar DAGOMO, wacce ke tallafawa jama'a masu yawan shekaru.

Darakta janar din kungiyar gwamnonin Arewan ya kara da cewa, "Dukkan ma'aikatan ofishin NGF an bukaci su killace kansu. Muna karfafa guiwar duk wadanda aka gayyata taron don gabatar da komai su yi hakan. Da abinda muka fara yi, muna fatan kara wa wasu kwarin guiwa a kan su killace kansu kafin su san matsayin lafiyarsu."

"A taron NGF da aka yi, duk wasu matakan da suka dace wadanda NGF suka bayyana, mun dauka. Amma ba zamu iya hasashen halin da lafiyarmu take ba. Zamu ci gaba da killace kanmu tare da bin dukkan ka'idojin kare jama'a daga samun cutar."ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel