Yanzu-yanzu: Mutane 6 da ke jinyar COVID-19 a Legas sun warke
- Majinyata shida da ke fama da cutar coronavirus a jihar Legas ne a yau suka warke
- Za a sallamesu daga cibiyar killace majinyatan cutuka masu yaduwa da ke Yaba a jihar
- Tunde Ajayi, mai bada shawara ta musamman ga gwamnan jihar Legas, ya bayyana hakan a shafinsa na twitter a yau Alhamis
Majinyata shida da ke fama da cutar coronavirus a jihar Legas ne a yau suka warke. Za a sallamesu daga cibiyar killace majinyatan cutuka masu yaduwa da ke Yaba a jihar.
Tunde Ajayi, mai bada shawara ta musamman ga gwamnan jihar Legas, ya bayyana hakan a shafinsa na twitter a yau Alhamis.
Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, ya rubuta: "Shida daga cikin majinyatan cutar COVID-19 ne suka warke kuma za a sallamesu nan ba da daewa ba. Abinda jihar Legas ke yi a yanzu ya sha banban. Mu ne a gaba."
Karin bayani zai biyo baya...

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Gwamnan APC ya nada yaro mai shekaru 15 a matsayin sarki mai daraja ta daya a jiharsa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng