Za a yi wa Ali Nuhu da wasu jaruman Kannywood 5 gwajin COVID-19

Za a yi wa Ali Nuhu da wasu jaruman Kannywood 5 gwajin COVID-19

Shahararren jarumin fina-finai, Ali Nuhu ya ce hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) za ta yi masa gwajin cutar coronavirus.

Jarumi Ali Nuhu tare da wasu 'yan Kannywood biyar na daga cikin taurarin da suka samu halartar bikin karrama jarumai da aka gudanar a Legas a ranar Asabar 14 ga watan Maris 2020.

Gwamnatin jihar Legas ta yi kira ga duk wandanda suka halarci bikin da su je a yi musu gwajin cutar coronavirus saboda an gano cewa akwai mai dauke da cutar cikin wadanda suka halarci bikin.

A hirar da fitaccen jarumi Ali Nuhu ya yi da BBC a daren yau Talata, ya ce jami'an hukumar NCDC sun samesa inda suka bukaci da ya bi su ofishinsu don yi masa gwajin cutar coronavirus.

Hakazalika, ya ce sun garzaya wajen abokan sana'arsa da suka samu halartar wurin bikin karrama taurarin don su ma a debi jininsu.

Abokan aikinsa din kuwa da suka samu halartar wurin sun hada da Ado Gwanja, Abubakar Maishadda, Hassan Giggs da wani mutum daya.

Za a yi wa Ali Nuhu da wasu jaruman Kannywood 5 gwajin COVID-19

Za a yi wa Ali Nuhu da wasu jaruman Kannywood 5 gwajin COVID-19
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Gwamnan APC ya nada yaro mai shekaru 15 a matsayin sarki mai daraja ta daya a jiharsa

Kamar yadda Ali Nuhu ya ce, za a gudanar da binciken jininsu din ne a daren nan sannan a sanar dasu sakamakonsu a ranar Laraba.

A halin yanzu dai, fiye da mutane arba'in ne a Najeriya suka kamu da mugunyar cutar nan ta coronavirus. A ciki kuwa har da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abba Kyari.

Akwai Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi da kuma Muhammad Atiku, dan hamshakin mai kudi, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar kujerar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar PDP a 2019, Atiku Abubakar.

A karon farko kuwa tun bayan barkewar cutar a Najeriya, an samu mutum daya da ya riga mu gidan gaskiya sakamakon cutar a ranar Litinin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel