Bidiyon yadda wani sanata ya cire takunkumin hanci kafin yayi tari

Bidiyon yadda wani sanata ya cire takunkumin hanci kafin yayi tari

- Anyi dariya babu kakkautawa a majalisar dattijan kasar nan bayan da Sanata Abdullahi Adamu ya cire takunkumin hancinsa don yi tari a zauren majalisar dattijai

- Tun bayan bullar annobar da fara yaduwarta a Najeriya, 'yan kasar suka dauka matakan kare kansu daga muguwar cutar ta hanyar amfani da safar hannu da kuma takunkumin fuska

- Amma kuma lamarin ya ba sanatoci da dama dariya yayin da Adamu ya cire wannan takunkumin na fuskarsa don tari a majalisar dattijan a ranar Talata

Anyi dariya babu kakkautawa a majalisar dattijan kasar nan bayan da Sanata Abdullahi Adamu, sanata mai wakiltar jihar Nasarawa ta yamma ya cire takunkumin hancinsa don yin tari a ranar Talata.

Mai dauke da muguwar cutar coronavirus kuwa zai iya yada cutar ta hanyar tari.

Tun bayan bullar annobar da fara yaduwarta a Najeriya, 'yan kasar suka dauka matakan kare kansu daga muguwar cutar ta hanyar amfani da safar hannu da kuma takunkumin fuska.

Ana amfani da takunkumin fuskar ne don kare sauran mutane daga samun duk abinda zai fito daga hanci ko baki na wani mutum daban.

Bidiyon yadda wani sanata ya cire takunkumin hanci kafin yayi tari

Bidiyon yadda wani sanata ya cire takunkumin hanci kafin yayi tari
Source: Facebook

KU KARANTA: Boko Haram: Dakaru 70 rundunar sojin Najeriya ta rasa a ranar Litinin

Amma kuma lamarin ya ba sanatoci da dama dariya yayin da Adamu ya cire wannan takunkumin na fuskarsa don tari a majalisar dattijan a ranar Talata, jaridar The Cable ta ruwaito.

Wannan lamarin kuwa yasa Sanata Sabi Abdullahi, wanda ya dau nauyin bukatar ya fara dariya tare da sauran wasu sanatocin.

Tarin ya iso ne a dai-dai lokacin da Yahaya Abdullahi, shugaban majalisar ke sanar da rasuwar Rose Oko, sanata mai wakilatar jihar Cross River ta Arewa.

A wani labari na daban, a kalla dakarun sojin Najeriya 70 ne suka rasa rayukansu sakamakon fatattakar tawagar 'yan ta'addan Boko Haram da suka yi a jihar Borno da ke yankin Arewa maso yamma na kasar nan, kamar yadda wata majiya daga jami'an tsaro ta tabbatar a ranar Talata.

Mayakan Boko Haram din sun harba makami mai linzami a kan wata mota ce da ke dauke da dakarun a yayin da motar ke tafiya a kusa da kauyen Gorgi a jihar Borno, kamar yadda wasu sojoji biyu suka sanar da AFP tare da bukatar sakaya sunayensu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel