Labari da dumi-dumi: An rufe kasuwanni a Legas saboda Coronavirus

Labari da dumi-dumi: An rufe kasuwanni a Legas saboda Coronavirus

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya bayar da umurnin rufe kasuwannin da ke jihar banda wadanda ake sayar da kayan abinci da magunguna.

Gwamnan ya bayar da wannan umurnin ne yayin wata taron manema labarai a kan Covid-19 wato Coronavirus a ranar Talata.

Ya ce ba zai yi wu a rufe dukkan kasuwanci ba a Legas saboda irin abinda zai faru da tattalin arzikin jihar amma za a dauki dukkan matakan da suka dace domin hana yaduwar cutar.

Labari da dumi-dumi: An rufe kasuwanni a Legas saboda Coronavirus

Labari da dumi-dumi: An rufe kasuwanni a Legas saboda Coronavirus
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Abba Kyari: Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya kamu da Coronavirus

Ya ce, "Na kuma sake zuwa a yau domin in sanar da ku halin da ake ciki game da Covid-19 a jihar Legas da kuma matakan da muke dauka domin yaki da cutar da ta jefa duniya cikin halin ha-ulai."

Gwamnan ya shawarci mazauna garin na Legas sun guji yin tafiya zuwa wasu jihohin kuma wasu da ke wasu jihohin su yi zamansu.

Sanwo-Olu ya ce gwamnatinsa za ta kafa kasuwar wucin gadi na sayar da abinci a makarantu.

Ya kara da cewa an bawa hukumomin tsaro da sauran hukumomin da suke da ruwa da tsaki a harkar su hukunta duk wanda aka kama yana karya dokar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel