Coronavirus: Zahra Buhari ta ce duniya ce ke tsarkake kanta

Coronavirus: Zahra Buhari ta ce duniya ce ke tsarkake kanta

- Diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zahra Indimi ta yi magana a kan wannan annobar coronavirus da ta addabi duniya

- Diyar shugaban kasar ta je kafar sada zumuntar zamani ta Instagram don yin jawabi ga mabiyanta

- Kamar yadda diyar shugaban kasan kuma matar hamshakin dan kasuwar ta bayyana, duniya tana tsarkake kanta ne

Labarin cutar coronavirus ta zama abin tsoro ga jama’a da dama a fadin duniya, ballantana kasashen nahiyar Afirka inda akwai matsala a fannin cibiyoyin kiwon lafiya. A kasashen ne manyan suke garzayawa kasashen turai don neman magani komai kuwa kankantar ciwon.

A halin yanzun kuwa, babu ta inda manyan za su garzaya Turai don neman magani sakamakon rufe filayen jiragen saman da aka yi, duk da dai can kasashen na fama da barkewar muguwar cutar.

Wannan annobar kuwa tana neman kawo kasashen duniya kasa ne don kasashe masu yawa sun rufe wuraren bauta da kuma na nishadi.

A Najeriya, labarin ya zama tamkar daga nesa amma a yau kuwa ya iso kusa don ta fara kama manyan mutane a kasar.

Coronavirus: Zahra Buhari ta ce duniya ce ke tsarkake kanta
Coronavirus: Zahra Buhari ta ce duniya ce ke tsarkake kanta
Asali: Instagram

DUBA WANNAN: Abba Kyari: Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya kamu da Coronavirus

Mutane da yawa a Najeriya sun yi magana a kan cutar nan amma wanda ba a dade da yi ba kuma ya ja hankulan jama’a, shine na Zahra Buhari.

Diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta je shafinta na Instagram inda ta bayyana ra’ayinta a kan annobar.

Kamar yadda ta bayyana, duniya ce ke tsarkake kanta da kuma abinda ke cikinta.

Babu jimawa ne aka tabbatar da cewa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi na dauke da kwayar cutar. An tabbatarwa da manema labarai hakan ne a yau Talata, 24 ga watan Maris ta hannun mataimakinsa na musamman a fannin yada labarai, Mukhtar Gidado ya fitar.

Hakazalika, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari ya kamu da cutar bayan ziyarar da ya kai kasar Jamus. A tabbatar da yana dauke da cutar ne a yau Talata, 24 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel