Labari da duminsa: Ma'aikatan Aso Villa 3 sun kamu da cutar Coronavirus

Labari da duminsa: Ma'aikatan Aso Villa 3 sun kamu da cutar Coronavirus

Rahoto daga TheNation na nuna cewa ma'aikatan ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban, Abba Kyari, guda uku sun kamu da cutar Coronavirus (COVID-19).

An yi yunkurin ji daga bakin masu magana da yawun shugaban kasa amma ba a samu nasara ba saboda gaba daya ba a ga Garba Shehu da Femi Adesina a fadar ba.

Majiya daga fadar shugaban kasan wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya tabbatar da cewa an shawarci dukkan mutanen da suka yi hulda da Abba Kyari.

Ya ce ana kyautata zaton cewa hakan yasa ma'aikatan fadar shugaban kasa basu zo aiki yau ba.

Bugu da kari, dukkan ma'aikatan mataimakin shugaban kasa, Yemo Osinbajo, basu shiga fadar ba a yau illa mai magana da yawunsa.

A yanzu dai, da alamun ana shirin kulle fadar shugaban kasar saboda an umurci dukkan dukkan ma'aikatan su koma gida.

Labari da duminsa: Ma'aikatan Aso Villa 3 sun kamu da cutar Coronavirus
Labari da duminsa: Ma'aikatan Aso Villa 3 sun kamu da cutar Coronavirus
Asali: UGC

Labarin mai inganci daga wakilinmu dake jihar Bauchi na nuna cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Kauran Bauchi, ya kamu da cutar Coronavirus.

A wani jawabin da mai magana da yawun gwamnan, Muhktar M Gidado ya saki, ya tabbatar da rahoton inda ya bukaci alumma su taimakawa gwamnan da addu'o'i.

Jawabin yace “Muna sanar da daukacin jama“a cewa sakamakon gwajin mutane shida da cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta gudanar kan gwamna Bala AbdulKadir Mohammed, iyalansa, da hadimansa da suka raka sa Legas ya fito.“

“Daga cikin sakamakon shida na mutum daya kadai ya tabbata ya kamu, kuma shine na Sanata Bala AbdulKadir Mohammed, gwamnan jihar Bauchi.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng