Yadda babbar kasuwar Kaduna ta koma bayan dokar El-Rufai a kan Coronavirus
Biyo bayan umarnin gwamnatin jahar Kaduna na hana bude kasuwanni a jahar, babbar kasuwar jahar Kaduna ta tunawa da babban Malami Sheikh Abubakar Gumi ta zama wayam.
Wannan na daga cikin matakan kandagarki da gwamnatin jahar ta dauka don kare yaduwar annobar cutar nan mai toshe numfashin dan Adam, watau Coronavirus a tsakanin al’ummar jahar.
KU KARANTA: Jerin manyan mutanen da suka yi cudanya da Abba Kyari kafin a tabbatar ya kamu da Coronavirus

Asali: Facebook
Wasu daga cikin matakan da gwamnan jahar, Nasir Ahmad El-Rufai ya dauka sun hada da garkame makarantu, dakatar da sallar juma’a, rufe wuraren shakatawa, hana manyan taruka da zasu tara jama’a.
Haka zalika Gwamna El-Rufai ya bada umarni ga ma’aikatan gwamnati daga mataki na 12 zuwa kasa dasu zauna a gida, sa’annan ya dauki alkawarin sanya dokar ta baci idan har hakan ne kadai hanyar da zata tabbatar da lafiyar jama’an jahar Kaduna.

Asali: Facebook
A wani labarin kuma, a kokarin ta na dakatar da yaduwar mugunyar annobar cutar nan mai toshe numfashin dan Adam, watau Coronavirus, gwamnatin tarayya ta baiwa ma’aikatanta hutun dole, inda ta nemi su yi aikin da za su iya yi daga gida.
Shugabar ma’aikatan Najeriya, Yemi Esan ce ta bayyana a ranar Litinin, 23 ga watan Maris cikin wata sanarwa da ta aika ma dukkanin ma’aikatun gwamnati.
Sanarwar ta bayyana cewa dukkanin jami’an gwamnatin tarayya daga mataki na 12 zuwa kasa su zauna a gida ba sai sun fita ofis domin aiki ba, haka zalika wadanda kuma lallai sai sun tafi wajen aiki toh su rage adadin bakin da ke kai musu ziyara.

Asali: Facebook
“Shi yasa ta umarci duk ma’aikata su dabbaka umarnin gwamnati da shawarwarin da take bayarwa game da yaki da annobar don kare yaduwar ta, da wannan ne muke umartar ma’aikata daga mataki na 12 zuwa kasa su yi zamansu a gida daga ranar Talata 24 ga watan Maris, har sai yadda hali ya yiwu.” Inji ta.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng