Jerin manyan mutanen da suka yi cudanya da Abba Kyari kafin a tabbatar ya kamu da Coronavirus

Jerin manyan mutanen da suka yi cudanya da Abba Kyari kafin a tabbatar ya kamu da Coronavirus

Mugunyar annobar nan mai toshe numfashi watau Coronvirus ta kama babban makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Najeriya, Malam Abba Kyari.

Premium Times ta ruwaito jaridar This Day ne ta fara wallafa labarin Abba Kyari ya kamu da cutar bayan an gudanar da gwaji a kansa da kuma maigidansa, shugaba Buhari, inda sakamakon gwajin ya nuna Buhari bai kamu da cutar ba.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kai ma jami’in dake yaki da Coronavirus hari a Nassarawa

Jerin manyan mutanen da suka yi cudanya da Abba Kyari kafin a tabbatar ya kamu da Coronavirus

Jerin manyan mutanen da suka yi cudanya da Abba Kyari kafin a tabbatar ya kamu da Coronavirus
Source: Twitter

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Abba Kyari ya dade a cikin kwamitin gudanarwar jaridar ThisDay, sai dai koda yake an tabbatar da kamuwar tasa, majiyoyin sun shaida a yanzu yana killace a gidansa, kuma baya cikin damuwa.

Majiyar ta shaida cewa Kyari ya kai ziyara kasar Jamus ne a ranar 7 ga watan Maris, inda ya dawo Najeriya bayan kwanaki 7, don haka ake ganin a can kasar ya dauko cutar, sakamakon kasar na fama da yaduwar cutar, wanda har ta kai ga shugaban kasar, Angela Merkel ta killace kanta.

Baya ga shugaban kasa Buhari wanda yake mu’amala da Abba Kyari a kai a kai, amma sakamakon gwaji ya nuna baya dauke da cutar, akwai wasu jerin manyan mutane da Kyarin ya yi cudanya dasu gabanin sanin matsayinsa, daga cikinsu akwai:

- Aliko Dangote

- Gwamna Aminu Bello Masari

- Gwamna Yahaya Bello

- Babban Sufetan Yansanda Muhammad Adamu

- Ministan lantarki Saleh Mamman

- Sakataren gwamnati Boss Mustapha

- Babagana Kingigbe

Bayan dawowarsa daga kasar Jamus, Kyari ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen taron daurin auren Hassan Adamu, dan babban sufetan Yansanda da aka gudanar a ranar 14 ga watan Maris a Abuja.

Haka zalika ya wakilcin shugaban kasa Buhari a wajen ta’aziyyar rasuwar mahafiyar gwamnan jahar Kogi, Yahaya Bello a garin Okene na jahar Kogi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel