Majalisar Dattijai za ta tafi hutu saboda Coronavirus

Majalisar Dattijai za ta tafi hutu saboda Coronavirus

Majalisar Dattawan Najeriya tana zama na musamman domin shirye-shiryen dakatar da zamanta na wani lokaci.

Rahotanni sun bayyana cewa dakatar da zaman ya zama dole ne domin kare yaɗuwar ƙwayar Coronavirus (COVID-19)

A cewar hadimin daya daga cikin shugabannin majalisar, "Majalisar ba ta da zabi sai dai dakatar da zamanta a yau."

Majalisar Dattijai za ta tafi hutu saboda Coronavirus
Majalisar Dattijai za ta tafi hutu saboda Coronavirus
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Abba Kyari ya kamu da Coronavirus

A makon da ya gabata ne majalisar da dakatar da ziyara zuwa harabar da kuma tarukan jin ra'ayin mutane.

A wani rahoton, kun ji cewa sakamakon gwajin da aka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari na Covid-19 ya nuna cewa shugaban baya dauke da kwayar cutar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Hukumar NCDC ta sanar da shugaban kasar cewa ba ya dauke da kwayar cutar a safiyar yau a Abuja.

A cewar wata majiya daga fadar shugaban kasa, gwajin da aka yi ya nuna cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari ya kamu da cutar kamar yadda sakamakon ya nuna a ranar Litinin.

Kyari ya tafi Jamus a ranar Asabar 7 ga watan Maris inda ya gana da wasu jami'an kamfanin Siemens a binrin Munich a kan shirin fadada aikin wutan lantarki a Najeriya.

Tuni dai shugaban ma'akatan fadar shugaban kasar ya killace kansa domin kada ya yada cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel