Coronavirus: Limaman Abuja sun goyi bayan Sultan kan rufe masallatai
- Kwamitin Limaman masallatai na babban birnin tarayya Abuja sun goyi bayan sarkin Musulmi, Abubakar Sa'ad III kan matakin rufe masallatai
- Limaman sun ce an dauki matakin ne domin kare yaduwar annobar cutar Coronavirus da a halin yanzu ta ke yaduwa a kasashen duniya
- Limaman sun shawarci al'umma su rika yin sallar jam'i a gidajensu da iyalansu ko wuraren aikinsu tare da adadin mutane kalilan
Kwamitin Limaman masallatai a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja (CFII) sun goyi bayan shugaban kwamitin koli na harkokin addinin musulunci (NSCIA) a kasar, Sultan Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III game da umurnin da ya bayar na rufe masallacin kasa da ke Abuja da sauran masallatai da ke birnin tarayyar.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Buhari bai kamu da Covid-19 ba, Abba Kyari ya kamu
Kwamitin, a cikin sanarwar da ta fitar a ranar Litinin mai dauke da sa hannun Sakataren ta, Ishaq Y. Zango ta ce an dauki matakin ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki a fanin da suka hada da likitoci da wasu manyan limamai da malamai, Grand Muftee Na Najeriya, Sheikh Sherif Ibrahim Saleh da shugabannin NSCIA.
Zango ya ce, "Muna goyon bayan kiraye-kirayen da ake yi na dakatar da yin sallar jam'i na taron jama'a masu yawa a dukkan masallatai da wuraren da ake sallah, ko da sallar Juma'a ce ko kuma sallolin farilla biyar na kowanne rana ko kuma rufe masallacin a inda akwai bukatar hakan domin kiyaye yaɗuwar mummunar annobar da ta fado wa al'umman duniya baki daya na ƙwayar cutar Covid-19 da aka fi sani da Coronavirus.
"Za mu iya yin Sallah ta jam'i tare da iyalan mu ko kuma tare da mutane kadan a gidajen mu ko ofisoshin mu", in ji Zango.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng