Abba Kyari: Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya kamu da Coronavirus

Abba Kyari: Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya kamu da Coronavirus

Sakamakon gwajin da aka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari na Covid-19 ya nuna cewa shugaban baya dauke da kwayar cutar kamar yadda Thisday ta ruwaito.

Hukumar NCDC ta sanar da shugaban kasar cewa ba ya dauke da kwayar cutar a safiyar yau a Abuja.

A cewar wata majiya daga fadar shugaban kasa, gwajin da aka yi ya nuna cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari ya kamu da cutar kamar yadda sakamakon ya nuna a ranar Litinin.

Kyari ya tafi Jamus a ranar Asabar 7 ga watan Maris inda ya gana da wasu jami'an kamfanin Siemens a binrin Munich a kan shirin fadada aikin wutan lantarki a Najeriya.

Yanzu-yanzu: Buhari bai kamu da Covid-19 ba, Abba Kyari ya kamu
Yanzu-yanzu: Buhari bai kamu da Covid-19 ba, Abba Kyari ya kamu
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Coronavirus: Jama'a sun tarwatse a ofishin Imigration bayan 'yar kasar China ta fadi warwas tana amai

Ya dawo gida Najeriya bayan sati daya a ranar Asabar 14 ga watan Maris amma babu alamun ya kamu da cutar.

Rahotanni sun bayyana cewa ya hallarci taron da aka gudanar a kan annibar Covid-19 a Najeriya a ranar Lahadi inda a nan ne ya fara tari.

Daga bisani ya mika kansa domin a yi masa gwaji kuma a jiya Litinin aka sanar da shi sakamakon gwajin.

Tuni dai Kyari ya killace kansa tun bayan da ya samu sakamakon gwajin.

Bayan fitowar sakamakon gwajin na Abba Kyari ya nuna yana dauke da cutar, an shawarci Buhari ya yi gwajin shima kuma aka gwada shi aka gano baya dauke da kwayar cutar kamar yadda wata majiya daga fadar shugaban kasa ta shaidawa TheCable.

A halin yanzu dai ba a tabbatar ko kamuwar Abba Kyari ce dalilin da yasa aka dakatar da yin taron mako-mako na majalisar zartarwa na kasa (FEC).

A halin yanzu akwai mutane 40 da suka dauke da kwayar cutar a Najeriya.

This Day ta ruwaito cewa a halin yanzu yana cikin koshin lafiya kuma ba ya nuna wasu alamun cutar illa dai tari da ya ke yi lokaci zuwa lokaci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel