Tashin hankali a fadar shugaban kasa bayan Gwamnan Bauchi ya killace kansa

Tashin hankali a fadar shugaban kasa bayan Gwamnan Bauchi ya killace kansa

- Waye da waye suka yi hannu da Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi, a lokacin da ya halarci taron zauren gwamnonin Najeriya a Abuja a makon da ya gabata

- Tun bayan da gwamnan ya bayyana cewa ya killace kansa bayan hannu da yayi da dan Atiku Abubakar mai suna Mohammed Atiku, manyan kasar nan hankulansu sun matukar tashi

- Asishana Okauru, darakta janar na zauren gwamnonin Najeriyar da kuma Abdulrazaque Bello-Barkindo, shugaban yada labarai da hulda da jama'a, duk sun halarci taron

Waye da waye suka yi hannu da Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi, a lokacin da ya halarci taron zauren gwamnonin Najeriya a Abuja a makon da ya gabata?

Tun bayan da gwamnan ya bayyana cewa ya killace kansa bayan hannu da yayi da dan Atiku Abubakar mai suna Mohammed Atiku, manyan kasar nan hankulansu suka matukar tashi.

Gwamna Mohammed dai ya halarci taron gwamnonin Najeriya wanda ya samu shugabancin Kayode Fayemi, gwamnan jihar Ekiti.

A taron wanda ya kai har tsakar dare, ya samu halartar gwamnoni da dama tare da mataimakan gwamnoni.

Asishana Okauru, darakta janar na zauren gwamnonin Najeriyar da kuma Abdulrazaque Bello-Barkindo, shugaban yada labarai da hulda da jama'a, duk sun halarci taron.

Washegarin ranar kuwa, gwamnan Bauchi ya sake halartar taron cin abincin safe da gwamnonin wanda suka yi da bankin duniya a Fraser Suites, wanda ke tsakiyar birnin kasuwancin tarayya da ke Abuja.

Tashin hankali a fadar shugaban kasa bayan Gwamnan Bauchi ya killace kansa

Tashin hankali a fadar shugaban kasa bayan Gwamnan Bauchi ya killace kansa
Source: UGC

KU KARANTA: Manyan kasashen duniya guda goma da suka fi farin ciki da jin dadin rayuwa

Hakazalika, gwamnan Bauchi ya halarci taron kwamitin tattalin arzikin kasar nan wanda mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya shugabanta.

Da yawa daga cikin wadanda suka halarci wadannan tarukan na bayyana damuwarsu sakamakon yuwuwar cewa sun shafi kwayar cutar a tarukan.

A ranar Litinin, Osinbajo ya dakatar da kaddamar da gidan rediyon tarayya wanda har yanzu bai bada dalili ba, duk da hakan zai iya kasancewa saboda matakan kariya ne.

A jiya ne takarda ta fito daga ofishin gwamnan jihar Bauchi, Gwamna Bala Mohammed a kan cewa ya killace kansa bayan ya hadu da dan Atiku wanda ya bayyana yana dauke da mugunyar cutar coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel