Yanzu-yanzu: Abba Kyari ya isa asibitin Gwagwalada don fara magance cutar COVID-19

Yanzu-yanzu: Abba Kyari ya isa asibitin Gwagwalada don fara magance cutar COVID-19

- Abba Kyari ya isa cibiyar killacewa ta Abuja da ke asibitin Gwagwalada don fara karbar magani

- Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar ya isa cibiyar ne da ke gefen babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja

- Na hannun damar shugaban kasar zai fara karbar maganin cutar COVID-19 ne a karkashin kular likitocin Najeriya

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, wanda a ranar Talata, 24 ga watan Maris aka tabbatar da cewa yana dauke da cutar coronavirus ya isa cibiyar killacewa ta babban birnin tarayyar kasar nan Abuja.

Kyari a halin yanzu zai fara karbar magani da agajin likitocin Najeriya ne cibiyar.

Wata majiya da ta sanar da jaridar Daily Sun a kan cewa daya daga cikin na’urorin amfanin marasa lafiyan an kaishi fadar shugaban kasar don amfanin Abba Kyarin, ba gaskiya bane.

A kalamansa: “Zan iya tabbatar da cewa babu wata na’urar da aka fitar. Dukkansu suna nan. Dayan a sashin masu bukatar taimakon a koda yaushe na asibitin ne inda dayan ke cibiyar kebancewar.”

Kyari dai yayi tafiya ne zuwa kasar Jamus a ranar Asabar, 7 ga watan Maris inda ya hadu da jami’an Siemens a Munich don wani shirin fadada wutar lantarkin Najeriya. Ya dawo Najeriya kuwa a ranar Asabar, 14 ga watan Maris.

Yanzu-yanzu: Abba Kyari ya isa asibitin Gwagwalada don fara magance cutar COVID-19
Yanzu-yanzu: Abba Kyari ya isa asibitin Gwagwalada don fara magance cutar COVID-19
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Bidiyon yadda wani sanata ya cire takunkumin hanci kafin yayi tari

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel