Covid-19: An hana ziyara sansanin 'yan gudun hijira a Borno

Covid-19: An hana ziyara sansanin 'yan gudun hijira a Borno

Gwamnatin jihar Borno ta hana mutane kai ziyara a sansanin 'yan gudun hijira (IDP) a fadin jihar na tsawon makonni hudu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar (SEMA), Hajiya Yabawa Kolo ce ta bayar da sanarwar a jiya inda ta ce an dauki matakin ne don kare cutar daga shigowa jihar.

Misis Kolo wace ke cikin tawagar Gwamna Zulum na kare yaduwar cutar ta bayar da sanarwar ne yayin wani ganawa da ta yi da manajojin sansanin 'yan gudun hijirar a Maiduguri babban birnin jihar.

Covid-19: An hana ziyara sansanin 'yan gudun hijira a Borno
Covid-19: An hana ziyara sansanin 'yan gudun hijira a Borno
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Coronavirus: Jama'a sun tarwatse a ofishin Imigration bayan 'yar kasar China ta fadi warwas tana amai

A makon da ya gabata ne Zulum ya nada mataimakinsa, Umar Kadafur a matsayin jagorar wata tawaga da za ta kare yaduwar cutar a jihar da ta kunshi hukumomi kamar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Kungiyoyin Lafiya, Ma'aikatar Lafiya, Ilimi, Sadarwa, Kananan hukumomi, Addinai da kungiyoyi masu alaka da ayyukan jin kan al'umma.

A cewar ta, jihar ta dauki matakin ne domin kare yaduwar cutar zuwa sansanin inda ta kara da cewa ya zama dole a yi hakan duba da cewa an samu bukkar cutar a kasashen da ke makwabtaka da jihar kamar Chadi da Kamaru.

Ta bayyana cewa duk da rufe iyakokin kasar da aka yi, ana samun mutane suna shigowa sansanin 'yan gudun hijirar.

Shugaban SEMA na Borno ya bawa shugabanin sansanin 'yan gudun hijira na Gamboru-Ngala, Damasak, Kalabalge, Banki, Bama da Monguno umurnin kada su karbi 'yan gudun hijira daka kasashen da ke makwabtaka da su.

Ta ce: "Mun san cewa akwai barazana sosai a kewaye da mu duba da cewa an samu bullar kwayar cutar a Kamaru da Chadi kuma muna da iyakoki da wasu garuruwa a kasashen.

Ba mu son mu kai matakin da za mu fara yin magani saboda ko kasashen da suka cigaba sun wahala wurin shawo kan annobar. A matakin mu, mu na daukan dukkan matakan da ya dace domin ganin cutar bai shigo jihar mu ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel