Covid-19: Gwamnatin Tarayya ta dakatar da taron FEC

Covid-19: Gwamnatin Tarayya ta dakatar da taron FEC

Gwamnatin tarayya a jiya ta dage taron mako-mako na majalisar zartarwa na kasa (FEC) da aka saba gudanarwa har illa masha Allahu.

Shugaban kwamitin yaki da Coronavirus na shugaban kasa kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustaphja ne ya bayyana hakan a Abuja yayin da ya ke zantawa da manema labarai a kan annobar ta Covid-19 da matakan da ake dauka don takaita yaduwar cutar.

Ya kuma ce an rufe dukkan iyakokin kasa na Najeriya baki daya.

Ya bayyana cewar annobar ta yadu a kasashe 192 inda a Afirka an samu wadanda suke dauke da kwayar cutar kimanin 390,000, kasashe 42 cikin 54 sun samu bullar cutar yayin da mutane 48 sun mutu.

Covid-19: Gwamnatin Tarayya ta dakatar da taron FEC
Covid-19: Gwamnatin Tarayya ta dakatar da taron FEC
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Coronavirus: Jama'a sun tarwatse a ofishin Imigration bayan 'yar kasar China ta fadi warwas tana amai

Ya ce, "Abinda gwamnati ta mayar da hankali a kai shine gwaji da gano masu dauke da kwayar cutar sannan a killace su domin kare yiwuwar yaduwar ta cikin al'umma."

Ya ce nan da kankanin lokaci za rufe tashohin jiragen ruwa na kasar bayan an kammala daukan matakan da suka dace.

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya ce jiragen da ke jigilar kayayyaki ne kawai da mutanen da ke gudunar da ayyukan da ke ake bukatarsu sosai za a bari su sauka a Najeriya.

Ministan Lafiya na kasa, Dakta Osagie Ehanire ya ce tuni an fara bincike na musamman a kan wanda ya kamu da cutar a Ekiti inda ake zargin wani dan Amurka ya mutu saboda coronavirus.

Ya ce sakamakon gwajin ya nuna dan Amurkan baya dauke da cutar da mai kula da shi amma direban da ya kai su Ekiti yana dauke da kwayar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel