Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin rufe dukkan iyakokin Najeriya

Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin rufe dukkan iyakokin Najeriya

Gwamnatin tarayya ta bada umurnin rufe dukkan iyakokin Najeriya na kasa na tsawon makonni biyu domin hana mutanen da ke dauke da cutar Coronavirus shigowa kasar.

Sakataren gwamnatin tarayya wanda shine shugaban kwamiti na musamman kan lamarin Coronavirus, Boss Mustapha, ya bayyana hakan da yammacin Litinin, 23 ga Maris, 2020.

Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki inda yace: "Bisa shawarar kwamitin yakar Coronavirus, shugaba Buhari ya bada umurnin daukan wadannan matakai:

i. Dakatad da taron majalisar zantarwa har sai an bukaci hakan

ii. Dage zaman masu ruwa da tsaki zuwa ranar Alhamis, 26 ga Maris, 2020

iii. Rufe dukkan iyakokin Najeriya na tsawon makonni hudu daga ranar 23 ga Maris, 2020."

Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin rufe dukkan iyakokin Najeriya
Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin rufe dukkan iyakokin Najeriya
Asali: UGC

A bangare guda, mai martaba sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad ABubakar ya bada umurnin kulle dukkan Masallatan birnin tarayya Abuja.

Hakazalika Shugabannin Masallacin kasa dake Abuja, sun sanar da dakatad da Sallolin Khamsu-Salawati da Juma'a a Masallacin tare da kulleta domin takaita yaduwar cutar Coronavirus da ta fara addaban Najeriya.

A jawabin da suka saki ranar Litinin, jagorancin Masallacin sun bayyana cewa fari daga yau (23 ga Maris), za'a kulle dukkan shaguna, gidajen abinci, da kasuwan dake makwabtaka da Masallacin.

Jawabin yace: "Dubi ga lamarin kiwon lafiyar kasa ta COVID19, jagororin masallacin kasa ta dakatad da Khamsu-Salawati, Sallar Juma'a, tarurruka, da duk wani ayyuka a Masallacin da harabarta."

"Har da Shagunan kasuwanci da gidajen abincin dake jikin Masallacin za'a kulle."

"Yayinda zamu cigaba da addu'a ga Allah ya yaye mana wannan annoba kuma ya shiryar damu, muna kira da mutane su bamu hadin kai da fahita kan wannan mataki."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng