Da dumi dumi: Surukar Atiku Abubakar da jikokinsa basu kamu da cutar Corona ba

Da dumi dumi: Surukar Atiku Abubakar da jikokinsa basu kamu da cutar Corona ba

Surukar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da jikokinsa sun sha da kyar bayan sakamakon gwaji ya tabbatar da cewa ba su dauke da annobar kwayar cutar Coronavirus.

Idan za’a tuna, a ranar Lahadi ne Atiku Abubakar ya sanar da cewa dan sa, watau Muhammad yana dauke da kwayar da cutar Coronavirus kuma an garzaya da shi asibitin koyarwa na gwagwalada inda aka kebance shi.

KU KARANTA: An samu karin sabbin alamomi dake bayyanar da Coronavirus a jikin dan Adam

Jaridar Punch ta ruwaito wannan yasa aka gudanar da gwajin cutar a jikin matarsa Badriyya da yayansu, kuma cikin ikon Allah sakamakon gwajin ya nuna basu dauke da kwayar cutar, amma dai suna nan a killace a gidansu dake rukunin gidaje na Taslee Palm City, titin Uruguay, Maitama Abuja.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Muhammad yana auren Badriyya ce, diyar tsohon gwamnan jahar Bauchi, kuma diyar tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Ahmad Adamu Muazu.

Mataimakin shugaban mazauna rukunin gidajen Taslee Estate, Alhaji Zakari Aliyu ya bayyana cewa babu wani abin firgici a yanzu, tunda dai hatta iyalansa basu kamu da cutar ba, sa’annan ya yaba ma matar bisa hadin kan da ta basu.

“Da misalin karfe 1 na dare aka tafi da mijinta, kuma sakamakon gwaji ya nuna yana dauke da cutar, amma sakamakon kuma ya nuna matarsa da yaransa basu dauke da ita, duk da haka an killace tsawon kwanaki 14 a gidansu.” Inji shi.

Shi dai Muhammad Atiku ya dawo ne daga kasar Switzerland, kasar da ita ma take fama da yaduwar cutar Coronavirus, sai dai Zakari yace ya kamata jama’a su sani yaran Atiku uku ne a rukunin gidajen Taslee.

Da wannan ne hukumar gudanarwar rukunin gidajen ta dakatar da shigowar yan aikin gidajen rukunin wadanda ba a cikin gidajen suke zama ba, haka zalika ta gargadi mazauna gidajen su rage adadin bakin da suke kai musu ziyara, sa’annan su rage cudanyar yaransu da abokansu na cikin rukunin.

A wani labarin kuma, masana kiwon lafiya a kasar Birtaniya, kwararru a sashin Kunne, Hanci da Makogwaro sun gano wasu sabbin alamomin cutar Coronavirus, daga ciki akwai daina jin dandano a harce da kuma daina gane kamshi ko wari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng