Coronavirus: An kulle Masallacin kasa dake Abuja

Coronavirus: An kulle Masallacin kasa dake Abuja

Shugabannin Masallacin kasa dake Abuja, sun sanar da dakatad da Sallolin Khamsu-Salawati da Juma'a a Masallacin tare da kulleta domin takaita yaduwar cutar Coronavirus da ta fara addaban Najeriya.

A jawabin da suka saki ranar Litinin, jagorancin Masallacin sun bayyana cewa fari daga yau (23 ga Maris), za'a kulle dukkan shaguna, gidajen abinci, da kasuwan dake makwabtaka da Masallacin.

Jawabin yace: "Dubi ga lamarin kiwon lafiyar kasa ta COVID19, jagororin masallacin kasa ta dakatad da Khamsu-Salawati, Sallar Juma'a, tarurruka, da duk wani ayyuka a Masallacin da harabarta."

"Har da Shagunan kasuwanci da gidajen abincin dake jikin Masallacin za'a kulle."

"Yayinda zamu cigaba da addu'a ga Allah ya yaye mana wannan annoba kuma ya shiryar damu, muna kira da mutane su bamu hadin kai da fahita kan wannan mataki."

Coronavirus: An kulle Masallacin kasa dake Abuja
Coronavirus: An kulle Masallacin kasa dake Abuja
Asali: Twitter

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta yi amfani da sojoji da 'yan sanda wajen tabbatar da cewa jama'a sun nesanta da junansu domin takaita yaduwar kwayar cutar coronavirus.

Ministan yada labarai da al'adu na kasa, Lai Mohammed, ne ya sanar da hakan yayin wata ganawarsa da manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Ministan ya ga baiken wasu jagorori da malaman addinai da suka yanke shawarar yin watsi da umarnin gwamnatin tarayya na hana taron jama'a masu yawa.

Wasu masallatai da coci-coci sun gudanar da taron ibada na ranar Juma'a da Lahadi kamar yadda suka saba duk da umarnin da gwamnati ta bayar na a rufe wuraren ibada a matsayin matakin dakile yaduwar kwayar cutar corona.

A cewar ministan, "gwamnatin tarayya tana sane da cewa wasu shugabannin addini da siyasa sun ki yin biyayya ga umarnin gwamnati na hana taron jama'a da yawa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel