Atiku: Gwamnan Bauchi ya yi gwaji, ya rufe kansa saboda yiwuwar yada Coronavirus

Atiku: Gwamnan Bauchi ya yi gwaji, ya rufe kansa saboda yiwuwar yada Coronavirus

Mun ji cewa akwai wadanda su ka hadu da Yaron tsohon mataimakin shugaban kasa, Muhammad Atiku Abubakar, wanda yanzu ya ke dauke da cutar COVID-19.

Labari ya zo mana daga Ladan Salihu cewa Mai girma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya na cikin wadanda su ka shiga jirgi guda da Muhammad Atiku Abubakar.

Gwamnan da Tawagarsa su na tare da Yaron Atiku Abubakar ne a cikin jirgin daga Garin Legas zuwa babban birnin tarayya Abuja. Gwamnan ya ce kawo yanzu garau ya ke.

Bayan isowar Alhaji Muhammad Atiku gida a Abuja ne aka fara zargin cewa ya na dauke da wannan cuta ta Coronavirus, an kuma tabbatar da haka bayan yi masa gwaji.

Shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamnan jihar Bauchi, Malam Ladan Salihu ya bayyana cewa babu shakka Bala Mohammed sun hadu da wannan Bawan Allah kwanaki.

KU KARANTA: Shugabannin kasashe sun killace kansu bayan haduwa da Masu COVID-19

Atiku: Gwamnan Bauchi ya yi gwaji, ya rufe kansa saboda yiwuwar yada Coronavirus

Gwamnan Bauchi ya nesanta kansa daga jama'a inji Hadiminsa
Source: Twitter

Har ila yau, Salihu ya tabbatar da cewa Mai girma gwamnan ya gaisa da Muhammad Atiku Abubakar, kuma sun yi musafaha, watau sun shafa hannun juna a lokacin.

Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa za a iya daukar wannan cuta yayin da aka gaisa da maras lafiya. Cutar COVID-19 ta kan dade kafin ta bayyana a jikin mutum.

A halin yanzu dai Sanata Bala Mohammed ya yi gwaji domin tabbatar da halin da ya ke ciki. Sauran Mukarraban gwamnatin jihar su ma duk sun dauki wannan mataki.

Kawo yanzu dai ana ta addu’ar ganin cewa sakamakon gwajin ya nuna Gwamnan da Tawagarsa ba su kai ga kamuwa da wannan cuta da ya zagaya kasashen Duniya ba.

Tsohon Mai magana da yawun baki da kuma Kwamishinan, ya shaidawa jama’a cewa Gwamna Mohammed ya killace kansa a halin yanzu, bayan aukuwar wannan lamari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel