An samu karin sabbin alamomi dake bayyanar da Coronavirus a jikin dan Adam

An samu karin sabbin alamomi dake bayyanar da Coronavirus a jikin dan Adam

Masana kiwon lafiya a kasar Birtaniya, kwararru a sashin Kunne, Hanci da Makogwaro sun gano wasu sabbin alamomin cutar Coronavirus, daga ciki akwai daina jin dandano a harce da kuma daina gane kamshi ko wari.

Kungiyar likitocin Kunne, Hanci da Makogwaro na kasar Ingila ne suka sanar da haka, inda suka ce wadannan alamomi suna bayyana ne a inda sanannun alamomin cutar basu bayyana a jikin mai dauke da kwayar cutar ba.

KU KARANTA: Kaico! Annobar Corona ta kashe mutane 100 cikin sa’o’i 24 a kasar Amurka

Don haka suka ce duk mara lafiyan dake fama da wadannan matsaloli biyu, akwai yiwuwar yana dauke da cutar Coronavirus, saboda an samu ire iren mutanen nan a kasashen China da Kudancin Koriya, inda suka kira alamomin ‘Anosmia.’

Shugaban kungiyar, Farfesa Claire Hopkins da Farfesa Nirmal Kumar ne suka fitar da sanarwar inda suka ce an fara samun ire iren almomin Anosmia a kasashen Faransa, Italy, Amurka da Birtaniya.

“Ire iren marasa lafiyan nan sun taimaka kwarai wajen yaduwar cutar Covid-19, sai dai har yanzu hukumomi basu dauki wadannan alamomi da muhimmanci ba saboda ba’a killace masu su ko a musu gwaji.” Inji Claire.

Don haka suka bayar da shawarar a fara amfani da wannan hanya don gane masu dauke da cutar Coronavirus amma basu tari ko atishawa. Shi ma Farfesa Kumar ya ce: “Kananan yara dake dauke da cutar basu nuna alamomi irinsu tari ko atishawa ko zazzabi.

“Amma suna iya kamu da matsalar rashin gane kamshi ko wari, wannan na nufin cutar ta mamaye hancinsu kenan.” Inji shi.

Daga karshe Kumar ya yi kira ga gwamnati ta kara musu yawan kayan kariya a matsayinsu na likitocin dake duba marasa lafiya, saboda a yanzu haka jami’ansu da dama sun kamu da cutar a sanadiyyar kulawa da masu cutar saboda karancin kayan kariya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng