Coronavirus: Gwamnatin jihar Kogi ta umurci ma’aikata su zauna gida

Coronavirus: Gwamnatin jihar Kogi ta umurci ma’aikata su zauna gida

Gwamnatin jihar Kogi a ranar Litinin ta shiga sahun jihohin da suka umurci ma’aikatan gwamnatin jihar suyi zamansu a gida na tsawon makonni biyu.

Gwamnatin ta yanke shawarar hakane domin takaita yaduwar cutar Coronavirus (COVID19) da ta addabi duniya.

Kwamishan labarai da sadarwan jihar, Kingsley Fanwo, ya ce umurnin ya fara aiki daga yau Litinin.

Jawabin yace “Gwamnan jihar, Alh Yahaya Bello, ta amince da shirin kowa yayi aiki daga gida domin tabbatar da cewa cutar bata yadu a ofishohin gwamnatin jihar ba.“

Coronavirus: Gwamnatin jihar Kogi ta umurci ma’aikata su zauna gida

Coronavirus: Gwamnatin jihar Kogi ta umurci ma’aikata su zauna gida
Source: Twitter

Mun kawo muku rahoton cewa an samu karin masu cutar Coronavirus biyar a Najeriya da safiyar yau Litinin, 23 ga Maris, 2020. Cibiyar NCDC ta tabbatar.

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta bayyana hakan ne a shafinta na Tuwita da safiyar Litinin, 23 ga Mairs misalin karfe 09:45 am.

Jawabin yace “An tabbatar da mutane biyar da suka kamu da COVID19: 2 in Abuja, 2 a Lagos & 1 a Edo. 2 sun dawo daga kasar Ingila.“

A yanzu ga adadin masu cutar a jihohi

Lagos- 24

FCT- 6

Ogun- 2

Ekiti- 1

Oyo- 1

Edo- 1

Jimilla: 35

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel