FG ta dage dokar hana kai kayayyakin man fetur garuruwan iyakoki
- Gwamnatin tarayya ta dage dokarta ta haramta kaiwa garuruwan da ke kusa da iyakokin kasar nan man fetur
- Shugaban hukumar kwastam ta a kasa,wacce Hameed Ali ke shugabanta, ya haramta kai dukkan kayayyakin man fetur gidajen mai da ke da nisan kilomita 20 zuwa iyakokin kasar nan
- Amma kuma, bayan watanni hudu da wannan dokar, gwamnatin tarayya ta yanke shawarar dage dokar ta hanyar amincewa gidajen mayuka 66 a yankunan samar da man fetur
Gwamnatin tarayya ta dage dokarta ta haramta kaiwa garuruwan da ke kusa da iyakokin kasar nan man fetur.
Idan zamu tuna, a ranar 6 ga watan Nuwamban 2019 ne kwamitin kula da iyakokin kasar nan wanda shugaban hukumar kwastam ta a kasa, wacce Hameed Ali ke shugabanta, ya haramta kai dukkan kayayyakin man fetur gidajen mai da ke da nisan kilomita 20 zuwa iyakokin kasar nan.
Amma kuma, bayan watanni hudu da wannan dokar, gwamnatin tarayya ta yanke shawarar dage dokar ta hanyar amincewa gidajen mayuka 66 a yankunan, samar da man fetur.
DUBA WANNAN: A karshe; Shugaba Buhari na wasa ya gabatar da jawabi ga 'yan Najeriya a kan coronavirus
Kamar yadda takardar da aka saka wa hannu a ranar 18 ga watan Maris, wacce Dimka V. D. ya saka hannu, aka kuma mika ta ga shugabannin hukumar na yankunan da abun ya shafa a jihohin Ogun, Kwara, Katsina, Akwa-Ibom, Kebbi, Lagos, Kano/Jigawa, Kebbi, Niger/Kogi, Sokoto/Zamfara da Cross river ta bayyana.
Takardar ta bayyana: "Ana amfani da wannan damar wajen sanar daku cewa ofishin babban mai bada shawara ga shugaban kasa a kan tsaron kasa, ta hannun shugaban kwastam na kasa a kan cewa anyi rangwame ga gidajen mayuka 66 da ke kusa da iyakokin kasar nan da su ci gaba da kawo kayayyakin man fetur.
"A don haka ake bukatarku da ku hada jai da shugabannkn yankunanku don tabbatar da cewa ba a waskad da man ba zuwa wata manufa daban."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng