Coronavirus: Jawabin shugaba Buhari ga 'yan Najeriya (Bidiyo)

Coronavirus: Jawabin shugaba Buhari ga 'yan Najeriya (Bidiyo)

- Bayan dogon lokacin da shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari ya dauka bai ce komai a kan muguwar cutar Covid-19 ba, daga baya yayi magana

- A dan gajeren bidiyon da shugaban yayi jawabi a kan cutar, ya ce suna aiki tare da ma'aikatar lafiya domin ganin sun kare 'yan kasa daga annobar coronavirus

- Wannan jawabin ya zo bayan kwanki kalilan da uwargidan shugaban kasar ta wallafa a shafinta na twitter cewa daya daga ciki 'ya'yanta mata ta dawo daga ingila kuma ta killace kanta

Bayan dogon lokacin da shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari ya dauka bai ce komai a kan muguwar cutar Covid-19, daga baya ya yi magana a kanta tare da jawabi kan matakan da gwamnatinsa ke dauka a kan yaduwar cutar.

A dan gajeren bidiyon da shugaban yayi jawabi a kan cutar, ya ce "Muna aiki tare da ma'aikatar lafiya domin ganin mun kare 'yan kasarmu daga annobar coronavirus."

Ya kara da cewa, "A matsayinmu na gwamnati, wannan ne abin da muka fi mayar da hankali a kai. Sakamakon hakan ne muke kira gareku a kan tabbatar cewa ku kiyaye dukkan hanyoyin kariya daga kamuwa da cutar."

Coronavirus: Jawabin shugaba Buhari ga 'yan Najeriya (Bidiyo)
Coronavirus: Jawabin shugaba Buhari ga 'yan Najeriya (Bidiyo)
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: A karshe; Shugaba Buhari na wasa ya gabatar da jawabi ga 'yan Najeriya a kan coronavirus

Wannan jawabin ya zo bayan kwanaki kalilan da uwargidan shugaban kasar ta wallafa a shafinta na twitter cewa daya daga ciki 'ya'yanta mata ta dawo daga ingila kuma ta killace kanta.

Hakazalika, uwargidan shugaban kasar ta bayyana cewa ta bai wa dukkan ma'aikatanta hutun makonni biyu bayan wasu daga cikinsu sun dawo daga ingila.

'Yan Najeriya kuwa sun dinga suka tare da caccakar shugaban kasar a kan halin shiru da yayi. Wasu daga cikin jama'a sun dinga zarginsa da nuna halin ko-in-kula a kan barkewar cutar a Najeriya.

Akwai yuwuwar wannan jawbin nasa kuma ya bude idanun wasu daga cikin 'yan kasar nan da ke karyata wanzuwar cutar tare da daukan matakan kare kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel