Kaico! Annobar Corona ta kashe mutane 100 cikin sa’o’i 24 a kasar Amurka

Kaico! Annobar Corona ta kashe mutane 100 cikin sa’o’i 24 a kasar Amurka

Annobar cutar Coronavirus na cigaba da yaduwa a duniya, musamman a kasar Amurka inda ta kashe akalla mutane 100 cikin sa’o’i 24, wanda hakan ya kawo adadin mace macen da aka samu a sanadiyyar annobar zuwa 289 a Amurka.

Babban asibitin John Hopkins ce ta bayyana haka bayan tattara bayanai game da cutar a kasar, inda ta ce akwai bullar cutar a kowanne jaha cikin jahohi 50 na kasar Amurka, sa’annan mace macen ya fi yawaita ne a jahar New York.

KU KARANTA: Muna aiki a kan allurai 20 da zasu magance annobar Coronavirus – Cibiyar WHO

Alkalumman bayanai daga asibitin John Hopkins sun bayyana cewa mutane 114 sun mutu a New York, 94 a Washington sai kuma 28 a California, bugu da kari alkalumman sun nuna mutane 30,000 ne suka kamu da cutar a Amurka.

A hannu guda, mai alfarma Sarkin Saudiyya, Sarki Salman bin Abdulaziz ya sanya dokar hana shige da fice a kafatanin kasar Saudiyya daga karfe 7 na dare zuwa 6 na safiyar kowanne rana na tsawon kwanaki 21 don rage yaduwar cutar Coronavirus.

Jaridar Alarabiya ce ta ruwaito kamfanin dillancin labaru na kasar Saudiyya ta fitar da sanarwar, wanda tace umarnin Sarkin zai fara aiki ne daga ranar Litinin, 23 ga watan Maris na shekarar 2020.

Sanarwar ta kara da cewa ma’aikatan kula da al’amuran cikin gida ce za ta tabbatar da dabbaka dokar tare da hadin kan hukumomin Soji, Yansanda da sauran hukumomin farin kaya da aikin tabbatar da bin doka ya shafa.

Gwamnatin ta nemi jama’a su zauna a gidajensu a lokacin dokar, kada wanda ya fito har sai ta kama, kamar domin duba lafiyarsu. Sai dai dokar ta daga kafa ga muhimman ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu.

A wani labarin kuma, shugabar kasar Jamus, Uwargida Angela Merkel ta killace kanta bayan gwaji ya nuna cewa likitanta wanda ya dubata a ranar Juma’a ya kamu da cutar Coronavirus.

Da wannan ne Angela ta killace kan ta domin kauce ma yada cutar ga sauran jama’a, sa’annan za ta jira na tsawon makonni 2 domin sanin ta kamu da cutar ba ko kuwa bata kamu da ita ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel