Annobar Coronavirus: Ka da wanda ya sake zuwa ofishin Yansanda – Sufetan Yansanda

Annobar Coronavirus: Ka da wanda ya sake zuwa ofishin Yansanda – Sufetan Yansanda

Babban sufetan Yansandan Najeriya, Mohammed Adamu ya yi kira ga yan Najeriya dasu dakatar da kai ziyarce ziyarce zuwa ofisoshin Yansanda da Caji ofis dake duk fadin Najeriya don gudun yaduwar cutar Coronavirus.

Punch ta ruwaito babban sufetan ya nemi yan Najeriya su daina zuwa caji ofis a wannan lokaci da annobar Coronavirus ta yi kamari, inda adadin masu cutar suka kai mutum 30, har sai matsalar ta yi sauki.

KU KARANTA: Muna aiki a kan allurai 20 da zasu magance annobar Coronavirus – Cibiyar WHO

Adamu ya bayyana haka ne ta bakin kaakakin rundunar Yansandan Najeriya, DCP Frank Mba, inda ya nemi yan Najeriya su kasance masu biyayya ga tsare tsaren da aka gindaya na kauce ma yaduwar cutar Carona a Najeriya.

Haka zalika babban sufetan Yansandan ya gargadi jami’an hukumar Yansanda da ga kama mutanen da basu ji ba basu gani ba, musamman ba tare da wani kwakkwaran hujja ba, musamman a wannan lokaci.

“Dole ne a rage kama mutane, sai dai wadanda suka aikata munana laifuka kamar su fashi da makami, ta’addanci, kisan kai da kuma sauran laifukan da doka ta haramta bata belin wanda ya aikata su.

“Babban sufeta ya bada umarnin a tantance duk mutumin da ya zama lallai sai an kama shi don tabbatar da ba shi da cutar, sa’annan ya nemi yan Najeriya su dakatar da ziyarar da suke kaiwa ofisoshin Yansanda a duk fadin kasar nan, sai dai idan ya zama dole.” Inji shi.

Daga karshe babban sufetan ya sanar da garkame dukkanin makarantun Yansanda dake fadin kasar nan, sa’annan ya umarci Yansanda su tabbata sun dabbaka umarnin gwamnati na hana cudanyar jama’a da dama a wuri daya.

A wani labarin kuma, wasu kiristoci dake bauta a cocin Victorious Army International Church sun sanya zare da wasu jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Legas yayin da suka yi kokarin dabbaka dokar hana taron jama’a da ya zarce mutum 30 a jahar don gudun yaduwar annobar Coronavirus.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 22 ga watan Maris a cocin dake layin Acme a yankin Ogbara inda mabiya addinin Kiristan suka ci zarafin jami’an Yansanda da wata yar jarida daga gidan talabijin na TVC, Ivy Kanu tare da mai daukan hotonta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel