Annobar Corona: Kiristoci sun yi fada da Yansandan da suka yi kokarin hanasu bauta a Legas

Annobar Corona: Kiristoci sun yi fada da Yansandan da suka yi kokarin hanasu bauta a Legas

Wasu kiristoci dake bauta a cocin Victorious Army International Church sun sanya zare da wasu jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Legas yayin da suka yi kokarin dabbaka dokar hana taron jama’a da ya zarce mutum 30 a jahar don gudun yaduwar annobar Coronavirus.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 22 ga watan Maris a cocin dake layin Acme a yankin Ogbara inda mabiya addinin Kiristan suka ci zarafin jami’an Yansanda da wata yar jarida daga gidan talabijin na TVC, Ivy Kanu tare da mai daukan hotonta.

KU KARANTA: Muna aiki a kan allurai 20 da zasu magance annobar Coronavirus – Cibiyar WHO

Punch ta ruwaito yan cocin sun kai ma Yansandan RRR hari ne a lokacin da suke daukan hotunan abubuwan dake faruwa a Cocin, inda suka kwace wayoyin salula guda biyu daga hannunsu, Samsung S8+ da Samsung J4.

“Kwamandan Yansandan RRR, DCP Olatunji Disu ya tilasta ma mambocin cocin Victorious Army International Church bin umarnin gwamnatin jahar Legas na dakatar da duk wani taro daya haura mutane 50 don kare yaduwar Coronavirus a jahar.

“Da misalin karfe 9 na safe jami’an suka isa cocin, amma sai mambocin Cocin suka garkame Cocin, daga bisani bayan sun bude kofar shiga Cocin sai suka shiga dukan Yansanda, tare da kwace wayoyinsu. Da magiya Disu ya nemi shuwagabannin Cocin su rage adadin masu zuwa bauta a cocin kamar yadda gwamnatin jahar ta bukata.” Inji Yansandan.

A wani labarin kuma, dan tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma tsohon dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar APC da PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya kamu da cutar annobar Coronavirus.

Alhaji Atiku Abubakar da kansa ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani na Facebook, a daren Lahadi, 22 ga watan Maris, inda yace tuni suka garzaya da dan nasa zuwa asibiti domin samun kulawa.

“Sakamakon gwaji ya tabbatar da Da na yana dauke da kwayar cutar Coronavirus, mun sanar da hukumar kula da yaduwar cututtuka ta Najeriya, kuma mun garzaya da shi zuwa asibitin koyarwa na Gwagwalada domin kulawa da shi.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel