A karshe; Shugaba Buhari na wasa ya gabatar da jawabi ga 'yan Najeriya a kan coronavirus

A karshe; Shugaba Buhari na wasa ya gabatar da jawabi ga 'yan Najeriya a kan coronavirus

Obinna Simon, wani dan Najeriya mai wasan barkwanci da ke matukar kama da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya saki wani jawabi ga 'yan kasa inda a cikinsa ya yi magana a kan bullar annobar kwayar cutar coronavirus.

Fitaccen mai wasan barkwancin, wanda aka fi sani da 'MC Tagwaye', ya saki jawabin ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke cigaba da guna-guni a kan jinkirin da shugaba Buhari ke yi wajen gabatar da jawabi ga 'yan kasa a kan annobar coronavirus.

Kamar yadda ya saba yin magana cikin kwaikwayon muryar Buhari, MC Tagwaye ya bukaci 'yan Najeriya su mayar da hankali wajen biyayya ga hanyoyin dakile yaduwar COVID-19.

A cikin sakon faifan bidiyon mai tsawon dakika 140 da ya wallafa a shafinsa na 'Tuwita' (@MC_Tagwaye), ya ce, "shugaba Buhari ya hana dukkan jami'an gwamnati fita kasashen waje tare da daukan matakan dakile yaduwar kwayar cutar corona a fadin kasa.

A karshe; Shugaba Buhari na wasa ya gabatar da jawabi ga 'yan Najeriya a kan coronavirus

MC Tagwaye
Source: Twitter

"Dukkan kasashen duniya sun dauki matakan ganin cewa kwayar cutar ba ta cigaba da yaduwa a kasashensu ba. An dauki mataki a kan cutar ne ba don a takurawa jama'a ba, sai don a karesu daga kamuwa da ita.

"Najeriya, kamar sauran kasashen duniya, ta dauki matakai daban-daban domin dakile kwayar cutar corona. Matakan sun hada da;

DUBA WANNAN: Coronavirus: Yadda fasinja ya jawo tashin hankula a filin jirgin sama na Legas

"Haramtawa jami'an gwamnati fita kasashen ketare da kuma hana jirage daga wasu kasashen duniya sauka a Najeriya. Bayan an dauki wasu sauran matakai a cikin gida domin hana kwayar cutar uaduwa."

Kalli faifan bidiyon:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel