Coronavirus: Yadda fasinja ya jawo tashin hankula a filin jirgin sama na Legas

Coronavirus: Yadda fasinja ya jawo tashin hankula a filin jirgin sama na Legas

Wani fasinja da zai je Asaba daga Legas ya tashi hankalin jama'a a ranar Asabar bayan an gano bashi da lafiya. An gano fasinjan na fama da muguwar rashin lafiya ne yayin da ake tantance shi a filin jirgi.

Wata majiya kusa da kamfanin jiragen Air Peace ta bayyana cewa ya kamata fasinjan ya yi tafiyar ne a ranar Litinin amma sai ya dage ta zuwa ranar sati saboda rashin lafiyarsa.

A ranar Litinin kuwa, kamfanin Air Peace ya tura jami'ansa a kowanne sako na filin jirgin don duba dumin jikin fasinjoji tare da basu sinadarin tsaftace hannaye. Duk wanda dumin jikinsa ba dai-dai ba ana tura shi asibitin filin jirgin.

Bayan duba dumin jikin fasinjan, jami'ai sun gano cewa yana fama da matsananciyar rashin lafiya sakamakon zafin jikinsa da yayi yawa.

Kamfanin jirgin saman sun kebe shi da gaggawa kuma sun sanar da NCAA, FAAN da kuma cibiyar lafiya ta filin jirgin saman.

Coronavirus: Yadda fasinja ya jawo tashin hankula a filin jirgin sama na Legas
Coronavirus: Yadda fasinja ya jawo tashin hankula a filin jirgin sama na Legas
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Yadda al'amura ke gudana a gidan tsohon sarki Sanusi II Legas bayan mako guda

Majiyar ta bayyana cewa fasinjan wanda a take aka hana shi tafiya, bai dade da dawowa daga Ingila ba kuma an kaishi asibiti ba tare da ya sanar da hukumomi ba.

Babban jami'ar ayyuka ta Air Peace, Toyin Olajide ta tabbatar da aukuwar lamarin tare da cewa ana duba mara lafiyan.

"Wani fasinja da aka gano ya shigo kasar nan daga UK an gano bashi da lafiya sakamakon tantancewar da ake yi a filin jirgin.

"An gano cewa ya kamata yayi tafiyar ne a ranar Litinin amma sai ya fasa zuwa Juma'a. Sakamakon tsaurin binciken lafiya da aka kafa a filayen jirgi, jami'ai sun zakulo shi. Kafin ya shigo cikin jama'a ne aka gano shi kuma aka yi zargin akwai abinda yake boyewa. Muna jinjinawa gwamnati a kan kokarinsu na datse yaduwar muguwar cutar a Najeriya. Muna hada kai da gwamnati don ganin cutar bata yadu a kasar nan ba. Muna godiya ga ma'aikatanmu wadanda suka dage wajen zakulo marasa lafiya," tace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel