Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga 26 a Katsina da Zamfara

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga 26 a Katsina da Zamfara

Headkwatan tsaro ta Najeriya ta ce dakarun sojoji na Operation Hadarin Daji a baya-bayan nan ta kashe kimanin 'yan ta'adda 26 a wurare daban-daban a jihohin Zamfara da Katsina.

Mukadashin Direkta na sashin hulda da kafafen yada labarai na hedkwatan tsaro, Brig Janar Benard Onyeuko ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a babban birnin tarayya Abuja.

Onyeuko ya ce dakarun sojojin bayan samun sahihan bayannan sirri sun kashe 'yan bindiga biyu a garurruwan Bindim da Koli a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Ya kara da cewa yayin sumamen da suka kai sun yi nasarar kwato harsashi guda 17 mai tsawon 7.62mm na AK 47 da kuma babur guda daya.

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga 26 a Katsina da Zamfara

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga 26 a Katsina da Zamfara
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Dattijuwa 'yar shekara 103 da ta kamu da Coronavirus ta warke (Hoto)

Onyeuko ya kuma kara da cewa sojojin yayin sintiri a Gando sun ceto mutane bakwai maza da mata biyu da 'yan bindigan suka yi garkuwa da su.

A cewarsa, an mika mutanen ga iyalansu yayin da sojojin kuma sun kwato shanu 42 da tumakai 38.

Onyeoku ya ce a halin yanzu sojojin suna kara mamaye yankin suna sintiri wanda hakan a cewarsa ya kafa karfafawa mutanen garuruwan gwuiwa.

Ya kuma bayyana cewa sojojin a ranar 19 ga watan Maris sun amsa kirar da aka musu na neman dauki a kan wasu 'yan bindiga da suka sace shanu a kusa da Gurbin Magarya da Garin Gado a karamar hukumar Jibia na jihar Katsina.

A cewarsa, an kashe 'yan bindigan 24 yayin musayar wuta an kuma kwato bindigu 47, kananan bindiga biyu da bindigun farauta uku.

Ya ce, "Ana kira ga al'umma su cigaba da tallafawa Rundunar Sojojin Najeriya da bayyanai masu sahihanci.

"Rundunar sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro za su cigaba da atisayen domin tabbatar da tsare lafiya da dukiyoyin 'yan Najeriya bisa tsari da hangen nesa irin na shugaban hafsohin tsaro, Gabriel Olonisakin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel