Allah mai yadda yaso da bayinsa: Ango ya mutu ranar daurin aurensa

Allah mai yadda yaso da bayinsa: Ango ya mutu ranar daurin aurensa

Wani bawan Allah da ake shirin daurin aurensa, Mister Samuel Yarling, a garin Jos ya mutu ya bar amaryarsa da iyalansu cikin dimuwa da damuwa.

An shirya daura auren ne a cocin ECWA Seminary a ranar 21 ga watan Maris amma kwatsam sai mutuwa ta yi halinta wadda hakan ya jefa iyalan ango da amarya cikin halin dimuwa.

An shirya daura auren marigayi Yarling ne da amaryarsa, Miss Helen Weze, ma'aikaciyar jinya a asibiti da a halin yanzu iyalan suka ce tana kwance a Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Bingham (BHUT) sakamakon kaduwa da ta yi game da rasuwar angon ta.

Manema labarai da suka tattauna da wani daga cikin 'yan uwan marigayi Yarling ya ce yana cike da koshin lafiya kafin rasuwarsa.

Allah sarki: Ango ya mutu a ranar da za a daura masa aure
Allah sarki: Ango ya mutu a ranar da za a daura masa aure
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An dena musabaha yayin gaisawa a jihohin Taraba da Imo saboda fargabar coronavirus

Ya bayyana cewa shi da marigayi angon sun tafi gidan 'yar uwansu ne misalin karfe 12 na dare domin su dako kayan da zai saka ranar auren inda ya fadi ya buge kansa a kasa ya kuji kadan.

Ya ce sun tafi wani shagon sayar da magunguna kusa da su inda aka duba raunin aka yi masa magani kuma suka tafi masaukin su inda za su kwana.

Da ya ke magantuwa kan abinda ya faru, majiyar ya ce misalin bayan awana daya da dawowarsu masaukin su sai marigayi Yarling ya fara amai babu kakautawa.

Ya ce hakan ya sa nan take ya kira mutane aka taimaka masa aka garzaya da shi asibitin koyarwa na jami'ar Bingham don a duba shi amma da isarsu aka tabbatar musu cewa ya riga mu gidan gaskiya.

Ya bayyana rasuwar a matsayin abu mai kidimarwa domin marigayi Yarling ya ta fada masa cewa lafiyarsa kalau amma kwatsam sai lamari ya canja kuma ya mutu a hannunsa.

Wani abokin marigayin da ya yi magana da manema labarai ya ce marigayin ya kasance yana da hidimdimunsa ranar Juma'a amma ya tafi ya huta domin ya karasa abubuwan da safe.

Mai magana da yawun 'yan sanda na jihar, ASP Uba Agaba ya ce ba sanar da su afkuwar lamarin ba amma za su gudanar da bincike a lokacin da manema labarai suka tuntube shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel