Yanzu-yanzu: Na daga auren diyata saboda Coronavirus - Sarkin Daura
Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk, ya dage daurin auren diyarsa saboda annobar Corona virus da ta Najeriya da duniya gaba daya.
Sarkin ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayinda yake jawabi ga Malaman addini, dakatai da masu gari a fadarsa dake masarautar Daura, jihar Katsina.
Ya ce an sanya ranar daurin auren Asabar, 28 ga Maris, 2020 amma an dage.
Sarkin ya yi kira alumma su kasance cikin tsafta da kuma nisantan juna domin takaita yaduwar cutar.
Bugu da kari, sarkin ya dakatad da suk taruwa da ake a garin Daura, wanda ya hada da Islamiyoyi, da wasanni har ila ma shaa Allahu.

Asali: Twitter
Al'umma da dama sun taru a fadar Sarkin Daura a ranar Asabar 21 ga watan Maris domin yin addu'a game da bullar mummunan cutar Coronavirus.
Sarkin Daura, Alhaji Umar Farooq a ranar Asabar ne ya jagoranci addu'ar ta musamman da aka gudanar game da bullar annobar kamar yadda Channels tc ta ruwaito.
Yayin addu'ar da aka gudanar a fadarsa, Sarkin mai shekaru 84 da haihuwa ya bukaci al'ummar sa su dauki ƙwayar cutar mai hatsari a matsayin gwaji daga Allah kuma ya bukaci su kara dage wa da addu'o'i a kan cutar da sauran cututtukan masu kisa da wuri.
A bangare guda, Ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya bayyana cewa an samu karin mutane 10 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya.
Ministan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita ranar Asabar, 21 ga watan Maris, 2020.
Yayinda bakwai aka samu a Legas, sauran ukun na birnin tarayya Abuja.
Yanzu dai akwai jimillar masu cutar 22 a Najeriya kuma an sallami biyu da suka samu sauki.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng