Coronavirus: Jama'a sun tarwatse a ofishin Imigration bayan 'yar kasar China ta fadi warwas tana amai

Coronavirus: Jama'a sun tarwatse a ofishin Imigration bayan 'yar kasar China ta fadi warwas tana amai

Wani dan kwarya-kwaryan wasan kwaikwayo ya faru a yau ranar Juma'a a ofishin Hukumar Kula da Shige da Fice na Najeriya inda wata mata 'yar asalin kasar China ta yanke jiki da fadi a kasa ta fara amai.

An gano cewar matar 'yar kasar China tana daya daga cikin mutane da dama da suka tafi ofishin domin sabunta fasfo din su ko neman biza.

Daily Trust ta ruwaito cewa wadanda suke ofishin a lokacin da lamarin ya faru akwai 'yan sanda da sojoji cikinsu kuma dukkan mutanen da suka tafi ofishin don neman fasfo sun tsere bayan sun hangi matar tana amai.

Daya daga cikin jami'in hukumar da ya nemi a sakayya sunansa saboda ba a bashi izinin magana da manema labarai ba ya ce ofishin ya washe wayam cikin 'yan mintuna bayan afkuwar lamarin.

Coronavirus: Jama'a sun tarwatse a ofishin Imigration bayan 'yar kasar China ta yi fadi warwas ta yi amai

Coronavirus: Jama'a sun tarwatse a ofishin Imigration bayan 'yar kasar China ta yi fadi warwas ta yi amai
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Labari da dumi-dumi: ICPC ta kama Obono-Obla a Abuja

Ya ce, "Matar ta zo ofishin ayyuka ne a kan batun biza. Ta saka abin rufe fuska da ta zo ranar Alhamis amma ba ta kammala abinda ta zo yi ba. Ta sake dawowa ranar Juma'a amma wannan karon ba ta saka abin rufe fuskan ba.

"A yayin da yi mata hidimomin da ya kai ta wurin sai ta fara jin jiri, ta fadi kasa warwas tana tari da amai.

"Dan uwana, kowa ya ya cika wandon sa da iska ne.

"Abinda ya fi muni shine 'yan uwanta sun so su dauke ta amma jami'an mu suka hana su. Mun saka kayan kiyaye kan mu sannan muka kai ta wani daki. Amma wadanda suka razana sun tafi gida suma al'umma galibi da suka zo yin hidimominsu ba su dawo ba tunda suka gudu."

Wani cikin wadanda suka ziyarci ofishin, John Madu, ya ce: "Na zo neman wasu bayannai ne amma da na ga mutane suna gudu sai nima ya tsere. Daga bisani an fada min cewa wata mata 'yar kasar China ne ta fadi tana amai. Abinda na ke tsoro shine ta ziyarci ofishin a jiya. Idan ya tabbata tana dauke da Coronavirus, ta yaya gwamnati za ta gano dukkan wadanda suka yi cudanya da ita.

"Mun yi sa'a mutanen da suka zo ofishin ba su da yawa saboda hana tafiye-tafiye da aka yi, a da adadin mutanen da suka saba zuwa nan ya fi haka sosai.

"Ya kamata gwamnati ta dauki mataki a kan wadannan 'yan kasar Chinan da suka cika ko ina a Legas."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel