Sarkin Daura ya jagoranci addu'a ta musamman domin Coronavirus

Sarkin Daura ya jagoranci addu'a ta musamman domin Coronavirus

Al'umma da dama sun taru a fadar Sarkin Daura a ranar Asabar 21 ga watan Maris domin yin addu'a game da bullar mummunan cutar Coronavirus.

Sarkin Daura, Alhaji Umar Farooq a ranar Asabar ne ya jagoranci addu'ar ta musamman da aka gudanar game da bullar annobar kamar yadda Channels tc ta ruwaito.

Yayin addu'ar da aka gudanar a fadarsa, Sarkin mai shekaru 84 da haihuwa ya bukaci al'ummar sa su dauki ƙwayar cutar mai hatsari a matsayin gwaji daga Allah kuma ya bukaci su kara dage wa da addu'o'i a kan cutar da sauran cututtukan masu kisa da wuri.

Sarkin Daura ya jagoranci addu'a ta musamman domin Coronavirus

Sarkin Daura ya jagoranci addu'a ta musamman domin Coronavirus
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Coronavirus: Babu wajen gwaji a yankuna 4 cikin 6 na kasar nan

Sarkin ya bayyana wannan cutar a matsayin fitina da ta fi ta Boko Haram kuma ya ce a ganinsa idan ta cigaba da yaɗuwa nan da watanni biyu kowa zai koma bara.

Ya kuma bawa dukkan malaman islamiyya da makamantun addini su rufe makarantun kamar yadda gwamnatin jihar ta bayar da umurni.

Umar ya kuma yi juyayin yadda tsoron barkewar annobar ta sanya mahukunta a kasar Saudiyya suka dakatar da yin aikin hajji da Umara na wannan shekarar.

A halin yanzu an tabbatar da mutane 12 da ke dauke da ƙwayar cutar a Najeriya inda a duniya akwai aƙalla mutane 250,000 da suka kamu da cutar kuma ta kashe fiye da 10,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel