Labari da dumi-dumi: ICPC ta kama Obono-Obla a Abuja

Labari da dumi-dumi: ICPC ta kama Obono-Obla a Abuja

Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta ce ta kama tsohon shugaban kwamitin shugaban kasa na musamman a kan dawo da kadarorin gwamnati (SPIP) a ranar Juma'a a Abuja.

Mai magana da yawun hukumar, Rasheedat Okoduwa ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwar inda ta ce an kama shi bayan ya kwashe watanni yana yunkurin tserewa hukuma.

Hukumar ta ayyana neman Obono-Obla ruwa a jallo bayan ya ki amsa gayyatar da ta masa domin ya amsa tambayoyi game da zargin almundunahar kudade da wasu laifukan.

Ta umurci jami'an ta su damko shi a duka inda suka same shi.

Labari da dumi-dumi: ICPC ta kama Obono-Obla a Abuja
Labari da dumi-dumi: ICPC ta kama Obono-Obla a Abuja
Asali: Twitter

Okoduwa ya ce an kama tsohon shugaban na SPIP ne a Aso Drive da ke allon Millenium Park a ranar Juma'a a Abuja.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta damke ma'auratan da ke taimaka wa masu garkuwa da mutane

Ta ce, "Ya zama dole jami'an hukumar ICPC su kama Obono-Obla duba da cewa an dade ana nemansa ruwa a jallo tun watan Oktoban shekarar da ta gabata saboda ya ki amsa gayyatar da aka masa lokuta da dama."

"Hukumar tana neman Obono-Obla ya zo ya wanke kansa daga zargin gabatar da takardun bogi da almundahar kudi da wasu laifufuka.

"ICPC ta dade tana nazarin zirga-zirgarsa na wasu lokuta kafin daga karshe suka yi nasarar kama shi a Aso Drive da ke allon Millenium Park a ranar Juma'a a Abuja."

Ta kara da cewa wanda ake zargin ya musanta dukkan tuhumar da ake masa inda ya ce nemansa ruwa a jallo da ICPC ke yi yunkuri ne kawai na zubar masa da mutunci da bata masa suna.

Ya kuma musanta cewa an gayyace shi ya amsa tambayoyi kafin a sanar da cewa ana nemansa ruwa a jallo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel