Labari da dumi-dumi: Ɗan Atiku Abubakar ya kamu da Coronavirus

Labari da dumi-dumi: Ɗan Atiku Abubakar ya kamu da Coronavirus

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, a zaben 2019 Atiku Abubakar ya sanar da cewa ɗan sa ya kamu da ƙwayar cutar Covid-19 da aka fi sani da Coronavirus.

Atiku ya sanar da hakan ne a shafinsa na dandalin sanda zumunta na Twitter a ranar Lahadi 22 ga watan Maris na 2020.

Ya rubuta, "Da na ya kamu da ƙwayar cutar Coronavirus."

DUBA WANNAN: Coronavirus: Jama'a sun tarwatse a ofishin Imigration bayan 'yar kasar China ta fadi warwas tana amai

A cewar tsohon mataimakin shugaban kasar na Najeriya, an garzaya da dan sa zuwa asibitin koyarwa na kwararru da ke Gwagwalada a birnin tarayya Abuja domin yi masa magani.

Ya kara da cewa, "An sanar da hukumar kula da Cututtuka masu saurin yaduwa ta Najeriya @NCDCGov kuma an kai shi asibitin koyarwa na kwararru da ke Gwagwalada a Abuja domin yi masa magani da kulawa da shi. Zan yi farin ciki idan za ku iya saka shi a addu'o'in ku. Ku cigaba da kiyaye wa domin Coronavirus gaskiya ne."

A wani rahoton, kun ji cewa a ranar yau Lahadi, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa na samu karin mutane uku masu dauke cutar coronavirus (COVID-19), yanzu adadin masu cutar a Najeriya sun kai 30 kamar yadda Hukumar takaita yaduwar cututtuka (NCDC) ta sanar da hakan da safiya Lahadi a shafin ra'ayi da sada zumuntarta na Tuwita.

Jawabin ya ce “An tabbatar da mutane 3 sun kamu da cutar COVID19 a Legas Najeriya.“

“Biyu matafiya ne daga kasar waje kuma dayan ya kwasa ne a jikin wani.“

“A yanzu dai 22 ga Maris, akwai mutane 30 da suka kamu a Najeriya kuma babu wanda yayi wafati.“

“Don sanin adadin wadanda suka kamu da cutar, ku garzaya http://covid19.ncdc.gov.ng“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel