An dena musabaha yayin gaisawa a jihohin Taraba da Imo saboda fargabar coronavirus

An dena musabaha yayin gaisawa a jihohin Taraba da Imo saboda fargabar coronavirus

Yin musabaha tsohon al'ada ce ta al'umma ke amfani da ita a wasu sassan duniya domin gaisuwa da sada zumunci idan sun hadu amma a halin yanzu an hana yin hakan a jihar Taraba sannan al'ummar jihar Imo sun fara kauracewa musabahar don fargabar Coronavirus.

Binciken da The Nation ta yi a jihar Imo ya nuna cewa mutane na daukan matakan kare kansu daga kamuwa daga cutar inda masu hotel suka samar da sinadarin kashe kwayoyin cuta da mutane za su wanke hannunsu kafin su shiga harabar su.

Shugaban masu otel-otel na jihar Imo, China Chukulwunyere ya ce sun dauki matakin ne domin kare kansu da abokan huldarsu daga kamuwa daga cutar.

Jihohin Taraba da Imo sun haramta musabaha yayin gaisawa saboda coronavirus
Jihohin Taraba da Imo sun haramta musabaha yayin gaisawa saboda coronavirus
Asali: Twitter

Ya ce duk cewa ba a samu bullar cutar a jihar ba, sun daura wa kansu alhakin kare kansu da kansu tunda an samu bullar cutar a kasar duba da cewa gwamnatin jihar ba ta sanar da tsare-tsaren da ta keyi game da cutar ba.

DUBA WANNAN: Yadda takalma suka tona wa wasu 'yan fashi da makami asiri a Zaria

A jihar Taraba, gwamnan jihar Darius Ishaku bayan dawowarsa daga Abuja inda ya shafe kwanaki 87 domin a duba lafiyarsa ya ce ya haramta yin musabaha tare da takaita zirga-zirga.

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, Ishaku ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da kayayyakin gwaje-gwaje a jihar.

Ya kara da cewa gwamnan jihar za ta cigaba da wayar da kan mutane kan yadda za su kare kansu daga kamuwa daga cutar.

Gwamnan ya ce: "Abu na farko shine a dena musabaha (duk da cewa ni kai wasu lokutan ina yi). Idan ka haɗu da wani, ku yi gaisuwa irin ta Indiyawa ba tare da musabaha ba."

Abin farko shine mu dena taba jikin juna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel