Yanzu-yanzu: An sallami dan Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya

Yanzu-yanzu: An sallami dan Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya

An sallami dan kasar Italiyan da ya jajubo cutar Coronavirus Najeriya an tabbatar ya samu sauki daga cutar, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwoolu, ya sanar.

Gwamnan ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita da yammacin Juma'a inda aka bayyana hotunan dan Italiyan, kwamishanan lafiyan jihar Legas, Akin Abayomi, da wasu jami'an kiwon lafiyan jihar.

Gwamnan yace: "A matsayina na kwamandan yaki da COVID-19, ina farin cikin sanar da ku cewa dan kasar Italiyan nan ya barrantu daga cutar"

"Bisa ga hadin kan gwamnatin jihar Legas da Ogun da kuma jami'an gwamnatin tarayya, mun samu nasarar rage yaduwar cutar zuwa ga mutum daya."

"Dan Italiyan ya amince da bamu samfurin farin jininsa (Plasma) kafin sallamarsa yau (Juma'a). Jinin na da muhimmanci wajen maganin cutar."

Yanzu-yanzu: An sallami dan Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya

An sallami dan Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya
Source: Facebook

Yanzu-yanzu: An sallami dan Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya

Coronavirus Najeriya
Source: Facebook

Yanzu-yanzu: An sallami dan Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya

Yanzu-yanzu: An sallami dan Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya
Source: Facebook

Mun kawo muku a baya cewa Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya ce dan kasar Italiyan da ya kawo cutar Coronavirus Najeriya ya murmure kuma za'a sallameshi daga inda aka killaceshi nan ba da dadewa ba.

Sakataren yada labaran gwamnan, Kunle Somorin, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin kamfanin Simintin, Lafarge PLC, karkashin jagorancin shugabanta, Khaleed El Dokani, a ofishinsa dake Oke-Mosan, Abekuta.

Yace: "Mara lafiyan yana cikin halin lafiya kuma za'a sallameshi nan ba da dadewa ba."

Gwamnan ya bayyana cewa cutar babbar kalubale ce ga jihar Ogun, a matsayinta na jihar manyan masana'antun Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel