Kare 'yan Najeriya daga COVID-19 shi muke baiwa fifiko - Buhari

Kare 'yan Najeriya daga COVID-19 shi muke baiwa fifiko - Buhari

Shugaban kasa Muhammad Buhari a ranar Juma'a ya jaddada cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen ganin ci gaban walwalar 'yan Najeriya ballantana a halin da duniya ta tsinta kanta a kwanakin nan.

Shugaban kasar ya sanar da wannan ne a yayin da ya karba bakuncin hukumar kula da aikin hajji ta kasa a Najeriya, NAHCON, a fadar shugaban kasa a Abuja.

Buhari yace: "Ina matukar farin ciki da kuke aiki tare da ma'aikatar lafiya a kan kare 'yan kasa daga kamuwa da COVID-19.

"Dole ne kuyi aiki tare da son tabbatar da tsaron mahajjata. A matsayinmu na gwamnati, wannan ne muke baiwa fifiko."

Shugaban kasar ya yi kira ga hukumar da ta tabbatar da cewa an samar da kayan kiwon lafiya ga mahajjata.

Buhari ya nuna farin ciki da a kan ayyukan hukumar ta yadda suka rage kashi 15 na kudin aikin hajji.

"Nayi farin cikin ganin yadda kuke kokarin rage kudin nan da shekara mai zuwa. Wannan abin jinjina ne ballantana ganin yadda ci gaban nan ya shafi tattalin arziki. Wannan abun zai matukar amfanar mahajjata tare da kara taimakawa tattalin arzikin Najeriya," yace.

Kare 'yan Najeriya daga COVID-19 shi muke baiwa fifiko - Buhari
Kare 'yan Najeriya daga COVID-19 shi muke baiwa fifiko - Buhari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kama wasu ma'aurata da laifin aikata jima'i a cikin mota

Amma kuma ya ja kunnensu a kan sadaukar da ingancin kwanciyar hankalin mahajjata, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

"A lokacin da kuke kokarin rage kudin kujera, dole ne ku tabbatar da inganci da walwalar da zaku samar wa mahajjatan saboda wannan ne alhakin da ya rataya a wuyan hukumar," yace.

Shugaban hukumar, Zikrullah Hassan, ya sanar da shugaban kasar cewa hukumar na kokarin ganin walwala da jin dadin mahajjatan Najeriya.

Ya ce gwamnatin kasar Saudi tana duban 'yan Najeriya ballantana ta yadda take bada wajen zama. Ya tabbatarwa shugaban kasar cewa mahajjata za samu walwalar da tafi wacce suke mora a shekara mai zuwa.

Hassan yace: "Da amincewarka a wannan shekarar, muna tunanin daukar dukkan nauyin wajen zaman mahajjata don a da jihohi ne ke dauka. Dabarar hakan kuwa shine zamu rage kudin kujera."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel