Mijina ya sakeni saboda kawai na tambaye shi ya bani izinin kwanciya da abokinsa

Mijina ya sakeni saboda kawai na tambaye shi ya bani izinin kwanciya da abokinsa

Wata mata 'yar Najeriya mai suna Linda ta fada cikin tashin hankali bayan ta bukaci kwanciya da abokin mijinta don samun juna biyu. Linda tayi hakan ne kuwa don ta samu rabo bayan aurenta na shekaru takwas ya kasa samar da haihuwa.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, lamarin ya faru ne a Agodo Egbe da ke yankin Ikotun ta jihar Leagsa inda suke zama.

Wannan bukatar kuwa ta jefa Linda cikin mummunan tashin hankalin da ya kai ga mutuwar aurenta, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

Kamar yadda Linda ta bayyana: "A halin yanzu ina zaune da 'yan uwana ne a Ikorodu ta jihar Legas. Ina ta aikawa mijina ban hakuri da neman yafiya a kan bukatar da na mika gabansa.

"Mijina Okey dan kasuwa ne babba don har kasashen duniya yake fita, yana shigo da kaya kala-kala. Yana da kadarori masu yawa a Legas da kuma Kudu maso gabas din Najeriya. Babban kalubalensa kuwa shine rashin haihuwa.

Mijina ya sakeni saboda kawai na tambaye shi ya bani izinin kwanciya da abokinsa

Mijina ya sakeni saboda kawai na tambaye shi ya bani izinin kwanciya da abokinsa
Source: Facebook

DUBA WANNAN: An kama wasu ma'aurata da laifin aikata jima'i a cikin mota

"Mun yi aure ne shekaru takwas da suka gabata amma har yanzu babu haihuwa. Mun je asibiti sannan fastoci da dama sunyi mana addu'ar samun rabo."

Likitoci sun sanar da mijina cewa kwayoyin halittarsa basu da karfin kyankyashe kwai kuma yana ta karbar magani amma har yanzu shiru kake ji.

Linda ta ci gaba: "Na shiga damuwa saboda rashin sanin makomata a bangaren haihuwa. Mijina yace ya gaji da shan magunguna don haka ya mayar da hankali wajen kasuwancinsa.

"Tun bayan da muka gane matsalarmu, na so karbar rikon yara amma ya hana ni. Na ce ya samo mana mafita amma shiru. Sai na bashi shawarar ko zan kwanta da abokinsa yadda zan samu ciki mu haihu amma sai rigima ta barke.

"Ya fara zargin cewa ina kwanciya da abokinsa ne shiyasa nake neman hanyar da zan halasta kwanciya da abokin shi. Daga nan ne kuwa ya fatattake ni tare da sakina."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel