Ya saba dirkata kuma yana bayan-gida a tukwane na idan ya sha giyarsa - Matar aure ta sanar da kotu

Ya saba dirkata kuma yana bayan-gida a tukwane na idan ya sha giyarsa - Matar aure ta sanar da kotu

Wata matar aure mai suna Mary Okunade, a ranar Juma'a ta roki wata kotun gargajiya da ke zaman ta a Ado-Ekiti ta rba aurenta da mijinta Tokunbo saboda mashayin giya ne kuma ya kan lakada mata duka lokaci zuwa lokaci.

Ma'auratan sun kwashe shekaru 25 da aure kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Matar auren ta shaidawa kotu cewa mijin ta ya lalata kofa da tagogin gidan. "Ban taba samun kwanciyar hankali ba a shekaru 25 na auren mu."

Miji na ba shi da aikin yi sai shan giya da yawon dare. "Ya kan yi bayan gida a cikin tukwanen girki na duk lokacin da ya fita waje ya yi tatil da giyansa ya dawo da daddare. Ya kwashe karafuna hudu cikin shida da na siyo ya sayar da su," a cewar matar.

Ta kuma yi ikirarin cewa mijin na ta baya kula wa da ita da kuma yaransu uku masu shekaru 24, 19 da 14.

DUBA WANNAN: Coronavirus: An hana masu gidajen haya karbar kudin haya a Uganda da Kenya

Yayin yanke hukunci, shugaban kotun, Misis Olayinka Akomolede, ta ce ta raba auren tunda Tokunbo ya ki amsa gayyatar da kotun ta yi masa lokuta da dama.

Akomolede ta kuma bayar da umurnin 'yar su mai shekaru 14 ya zaune tare da mahaifiyar da ta shigar da karar yayin da sauran 'ya'yan masu shekaru 19 da 24 suna da zabin wanda za su zauna tare da shi.

Ta kuma bayar da umurnin Tokumbo ya rika bawa tsohuwar matarsa N6,000 duk wata domin kulawa da 'yar su mai shekaru 14.

"Ya kuma dawo da karafuna guda hudun da ya karbe daga hannun wanda ta yi karar," in ji shugaban kotun.

Wanda aka yi karar yana da ikon ganin diyarsa mai shekaru 14 in ji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel