Yanzu-yanzu: WAEC ta dage zana jarabawar wannan shekara

Yanzu-yanzu: WAEC ta dage zana jarabawar wannan shekara

Hukumar jarrabawan Afrika ta yamma, WAEC, ta dage zana jarabawar wannan shekara na daliban sakandare da aka shirya yi ranar 6 Afrilu, 2020.

Shugaban ofishin hukumar na Najeriya, Patrick Areghan, ya ce an dau matakin ne sakamakon kulle makarantun gwamnati da na kudi saboda takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Patrick Areghan: “Yanke shawaran na nuna yadda hukumar ke biyayya ga dokoki da umurnin gwamnatin Najeriya da gwamnatocin sauran kasashen Afrika ta yamma domin takaita yaduwar cutar."

"Bugu da kari, hukumar ta soke jadawalin gudanar da jarabawan sai ila ma shaa'a Llahu."

"Muna tabbatarwa dalibai, makarantu, masu ruwa da tsaki da kuma daukacin al'ummar cewa lamarin lafiya na sauki za'a dawo da jarabawan."

"Muna kira ga shugabannin makaranta su sanar da dalibansu wannan mataki."

Yanzu-yanzu: WAEC ta dage zana jarabawar wannan shekara
Yanzu-yanzu: WAEC ta dage zana jarabawar wannan shekara
Asali: Facebook

Hukumar majalisar dinkin duniya dake kula da kiwon lafiya, watau World Health Organization, WHO ta bayyana cewa a yanzu haka tana aikin sarrafa wasu allurai guda 20 da ka iya magance annobar cutar Coronavirus.

Jaridar Punch ta ruwaito wakiliyar WHO a kasar Rasha, Melita Vujnovic ce ta bayyana haka inda tace cibiyar WHO ta samu takardun neman tabbatar da ingancin magani tare da izinin gudanar da gwaji daga kamfanoni 40 da suka samar da allurai 20.

KU KARANTA: Jama’a sun karar da ‘maganin’ Coronavirus a Abuja da jahar Legas

Vujnovic ta bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Spuntik a ranar Juma’a, inda tace: “A yanzu haka kamfanoni 40 sun aiko ma WHO bukatar neman izinin yin gwajin wasu allurai 20, kuma wasu ma na cigaba da kirkiro wasu magungunan wanda a yanzu haka an fara gwada su, muna sa ran samun sakamakon farko a makonni masu zuwa.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel