An kama wasu ma'aurata da laifin aikata jima'i a cikin mota

An kama wasu ma'aurata da laifin aikata jima'i a cikin mota

- ‘Yan sandan kasar Italiya sun damke wasu ma’aurata da suke saduwa a cikin mota tare da yin karantsaye ga dokar kebancewa ta coronavirus

- Ma’auratan an gano cewa mijin dan asalin kasar Egypt ne mai shekaru 23 sai kuma matar ‘yar asalin kasar Tunisia ce mai shekaru 40

- Karin rahoto a kan hakan ya bayyana cewa dokar kebancewa da aka saka ta coronavirus ta haramtawa mutane biyu zama a waje daya a cikin mota

‘Yan sandan kasar Italiya sun damke wasu ma’aurata da suke saduwa a cikin mota tare da yin karantsaye ga dokar kebancewa ta coronavirus.

Ma’auratan da aka gano mijin dan asalin kasar Egypt ne mai shekaru 23 sai kuma matar ‘yar asalin kasar Tunisia ce mai shekaru 40. An kama su ne a kan titin Mecenate da ke birnin Milan, inda cutar coronavirus ta fi barkewa.

Kamar yadda jaridar Daily Mail UK ta wallafa, wnai dan sanda ne da ke bakin aiki ya kama ma’auratan.

Karin rahoto a kan hakan ya bayyana cewa dokar kebancewa da aka saka ta coronavirus ta haramtawa mutane biyu zama a waje daya a cikin mota.

An kama wasu ma'aurata da laifin aikata jima'i a cikin mota
An kama wasu ma'aurata da laifin aikata jima'i a cikin mota
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Coronavirus: Shugaba Buhari ya halarci sallar Juma'a a masallaci

Amma kuma ko a yayin sanar da dokar, ba a tabbatar da cewa za a hukunta ma’aurata ba a kan hakan.

Kasar Italiya ta bayyana a cikin daya daga cikin kasashen da mugunyar cutar coronavirus ta addaba a duniya. Hakan kuwa yasa aka rufe kasar don gudun yaduwarta.

‘Yan kasar Italiya na iya fita ne kadai daga gidajensu don siyan abinci ko kuma samun taimakon masana kiwon lafiya.

Dan kasar ne kuma mutum na farko da ya shigo Najeriya dauke da muguwar cutar. Bayan killacesa tare da bashi magani, ya warke daga muguwar cutar.

Mutane 3,526 ne na kasar Italiya suka kamu da cutar a cikin kwanakin nan. Hakan yasa masu cutar a kasarr suka ka 31,506. Amma an samu mace-macen mutane 2,503 na jama’a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel