Muna aiki a kan allurai 20 da zasu magance annobar Coronavirus – Cibiyar WHO
Hukumar majalisar dinkin duniya dake kula da kiwon lafiya, watau World Health Organization, WHO ta bayyana cewa a yanzu haka tana aikin sarrafa wasu allurai guda 20 da ka iya magance annobar cutar Coronavirus.
Jaridar Punch ta ruwaito wakiliyar WHO a kasar Rasha, Melita Vujnovic ce ta bayyana haka inda tace cibiyar WHO ta samu takardun neman tabbatar da ingancin magani tare da izinin gudanar da gwaji daga kamfanoni 40 da suka samar da allurai 20.
KU KARANTA: Jama’a sun karar da ‘maganin’ Coronavirus a Abuja da jahar Legas
Vujnovic ta bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Spuntik a ranar Juma’a, inda tace: “A yanzu haka kamfanoni 40 sun aiko ma WHO bukatar neman izinin yin gwajin wasu allurai 20, kuma wasu ma na cigaba da kirkiro wasu magungunan wanda a yanzu haka an fara gwada su, muna sa ran samun sakamakon farko a makonni masu zuwa.”
Ta kara da cewa kasar Rasha na yin duk mai yiwuwa don gudanar da gwajin allurai a kan cutar coronavirus tare da sanya idanu a kan dukkanin wadanda suka yi mu’amala da masu dauke da cutar don kare yaduwarta.
Ta kara nanata muhimmancin dakatar da dukkanin wasu gangamin wasannin motsa jiki da bukukuwan al’adun gargajiya da ka iya janyo cudanya tsakanin jama’a, don haka ta nemi kasashe su killace duk wanda aka ga alamun cutar da shi, a yi masa gwaji, a kula da shi don kare yaduwarta.
A wani labarin kuma, uwar kungiyar likitocin Najeriya, NMA ta umarci yayanta a jahohin Kaduna, Gombe, Ribas da babban birnin tarayya Abuja da su janye yajin aikin da suka shiga domin su taimaka wajen yaki da annobar Coronavirus.
Shugaban kugiyar, Dakta Francis Faduyile ne ya bayyana haka a ranar Juma’a yayin da yake ganawa da manema labaru a Abuja a ranar Juma’a inda yace wannan umarni na daga cikin matakan da NMA ta dauka domin shawo kan Coronavirus.
“Mun umarci dukkanin kungiyar NMA ta kowacce jaha ta kafa kwamitin mutane 5 da suka hada da likitoci, jami’an jinya, jami’an sarrafa magani don su sanya idanu akan matsayin aikin da ake gudanarwa a asibitocinmu.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng