Annobar Corona: Yahaya Bello ya hana gangamin mutum 30, ya kulle makarantu a Kogi

Annobar Corona: Yahaya Bello ya hana gangamin mutum 30, ya kulle makarantu a Kogi

A kokarinta na dakatar da yaduwar cutar nan mai toshe numfashin dan Adam watau Coronavirus, gwamnatin jahar Kogi a karkashin jagorancin Gwamna Yahaya Bello ta sanar da kulle dukkanin makarantu a duk fadin jahar daga ranar Litinin, 23 ga watan Maris.

Jaridar Premium Times ta ruwaito gwamnatin ta bayar da umarnin rufe makarantun gwamnati da makarantun kudi a jahar har sai baba ta ji kamar yadda shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jahar, Onogwu Muhammed.

KU KARANTA: Annobar Corona: Jerin Jahohi 13 a Najeriya da suka rufe makarantu tare da hana taron jama’a

Mista Muhammed ya bayyana haka ne a garin Lokoja a ranar Juma’a, inda ya ce an dauki matakin ne domin kare yaduwar cutar musamman a tsakanin malamai da dalibansu, da kuma kafatanin al’ummar jahar gaba daya.

Sanarwar ta ce umarnin ya shafi makarantun Firamari, Sakandari da kuma na gaba da sakandari, haka zalika gwamnatin jahar ta haramta duk wani taro daya haura na mutane 30 a dukkanin sassan jahar.

Gwamna Bello yace sun dauki wannan mataki ne kasancewa jahar Kogi mahada ga matafiya dake shiga da fice a yankunan Arewacin Najeriya da kudancin Najeriya, don haka ya nemi jama’a su baiwa gwamnati hadin kai domin a kare yaduwar cutar.

Haka zaika ya nemi jama’a su wanke hannuwansu da sabulu da ruwa, yayin da gwamnati ta samar da sansanin killace duk wadanda aka ga alamun kamuwarsu da cutar, bugu da kari ta tanadi jami’an bada agaji masu jiran ko-ta-kwana.

Har ila yau gwamnatin jahar Kogi na cigaba da wayar da kawunan jama’a game da illar cutar a tashoshin mota, kasuwanni da kuma unguwanni da kuma ta kafafen watsa labaru. Ga wasu lambobi da gwamnatin ta hayar 08064469625, 08030607102, 08034732988 da kuma 08076288933.

A wani labarin kuma, uwar kungiyar likitocin Najeriya, NMA ta umarci yayanta a jahohin Kaduna, Gombe, Ribas da babban birnin tarayya Abuja da su janye yajin aikin da suka shiga domin su taimaka wajen yaki da annobar Coronavirus.

Shugaban kugiyar, Dakta Francis Faduyile ne ya bayyana haka a ranar Juma’a yayin da yake ganawa da manema labaru a Abuja a ranar Juma’a inda yace wannan umarni na daga cikin matakan da NMA ta dauka domin shawo kan Coronavirus.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel