Kungiyar Likitoci ta umarci likitocin Kaduna da Abuja su koma bakin aiki don yaki da Corona

Kungiyar Likitoci ta umarci likitocin Kaduna da Abuja su koma bakin aiki don yaki da Corona

Uwar kungiyar likitocin Najeriya, NMA ta umarci yayanta a jahohin Kaduna, Gombe, Ribas da babban birnin tarayya Abuja da su janye yajin aikin da suka shiga domin su taimaka wajen yaki da annobar Coronavirus.

Shugaban kugiyar, Dakta Francis Faduyile ne ya bayyana haka a ranar Juma’a yayin da yake ganawa da manema labaru a Abuja a ranar Juma’a inda yace wannan umarni na daga cikin matakan da NMA ta dauka domin shawo kan Coronavirus.

KU KARANTA: Annobar Corona: Jerin Jahohi 13 a Najeriya da suka rufe makarantu tare da hana taron jama’a

“Mun umarci dukkanin kungiyar NMA ta kowacce jaha ta kafa kwamitin mutane 5 da suka hada da likitoci, jami’an jinya, jami’an sarrafa magani don su sanya idanu akan matsayin aikin da ake gudanarwa a asibitocinmu.

“Kwamitin zai yi gana da kwamitoci daban daban da gwamnonin jahohin suka kafa da wanda ministan Abuja ya kafa, da wannan ne muka umarci yayan kungiyar NMA dake yajin aiki a jahohi su janye, mu kuma daga sama zamu shiga rikicin kuma zamu gana da gwamnoninsu.

“Don haka kungiyar kananan likitoci, dake Abuja, Gombe, ESUT-Parklane da Kaduna, tare da NMA reshen jahar Ribas su dakatar da yajin aikinsu, su koma bakin aiki don kulawa da yan Najeriya, hakan ya zama wajibi domin kulawa da yan uwanmu ba tare da la’akari da cin kashin da ake mana ba.

“Amma fa NMA ba za ta saurara ma duk gwamna ko gwamnatin da ta ki rama mana biki a lokacin da bukatar ta ba, bayan mun samu galaba a kan Covid 19.” Inji shi.

Daga karshe yayi kira ga gwamnatocin jahohi sutabbata sun samar da kayan kariya ga likitoci yayin da suke bakin aiki ta yadda zasu gudanar da aikinsu cikin nutsuwa ba tare da tsoro ba.

A wani labarin kuma, a kokarinta na dakatar da yaduwar cutar nan mai toshe numfashin dan Adam watau Coronavirus, gwamnatin jahar Kogi a karkashin jagorancin Gwamna Yahaya Bello ta sanar da kulle dukkanin makarantu a duk fadin jahar daga ranar Litinin, 23 ga watan Maris.

Gwamnatin ta bayar da umarnin rufe makarantun gwamnati da makarantun kudi a jahar har sai baba ta ji kamar yadda shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jahar, Onogwu Muhammed.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel