Tsoron coronavirus: An mika wani mutum asibiti bayan ya sha 'magani' fiye da misali

Tsoron coronavirus: An mika wani mutum asibiti bayan ya sha 'magani' fiye da misali

- An mika wani dan Najeriya asibiti rai a hannun Ubangiji bayan ya sha magani ba bisa ka’ida ba don tsoron cutar Coronavirus

- Wani mai amfani da kafar sada zumuntar zamani ta twitter ne mai suna @Aprokodoctor ya wallafa labarin

- Ya bayyana cewa dama can magunguna guba ne, shan su dai-dai kadai shi ke sa su yi amfanin da ya dace a jikin dan Adam

An mika wani dan Najeriya asibiti rai a hannun Ubangiji bayan ya sha magani ba bisa ka’ida ba don tsoron cutar Coronavirus.

Wani mai amfani da kafar sada zumuntar zamani ta twitter ne mai suna @Aprokodoctor ya wallafa labarin.

Ya rubuta: “Yanzu-yanzu an kai wani mutum asibiti rai a hannun Ubangiji. Ya je ya sha kwayoyin maganin chloroquine ne saboda an ce yana maganin cutar coronavirus. Kowanne magani dai guba ne, gaskiya ayi amfani da hankali,”

Ya kara da cewa: “Tabbas chloroquine ya bayyana a matsayin babban magani ga wasu masu dauke da cutar Covid-19. Amma har yanzu ana ci gaba da gwada maganin ne kafin a fitar dashi a matsayin sahihin maganin cutar. Kowanne magani na da ilolinsa don haka ba kowanne ake hadiya ba,”

Tsoron coronavirus: An mika wani mutum asibiti bayan ya sha 'magani' fiye da misali
Tsoron coronavirus: An mika wani mutum asibiti bayan ya sha 'magani' fiye da misali
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yadda takalma suka tona wa wasu 'yan fashi da makami asiri a Zaria

Amma kuma likitan ya ci gaba da bayyana illolin chloroquine.

“A game da chloroquine, illolinsa sun hada da makanta, ciwon kai, jiri, raguwar bugun zuciya, suma, har da mutuwa. Tabbas duk abinda zai iya maganin cuta, zai iya kashe mutum. Na san ya ji tsoro ne wanda kowa zai iya yin abinda yayi.” ya ce.

“Har yanzu dai ana cigaba da bincike a kan yawan da mutum zai sha. Kada kayi tunanin cewa yadda ake shan na zazzabin cizon sauro duk daya ne. Idan mutum ya sha a yanzu, yana yin gwaji ne da rayuwarsa. Ba kowa ke da sa’ar bada labari ba,” ya kara da cewa.

Tuni dai gwamnatin Najerya ta dauka matakan gaggawa wajen ganin ta shawo kan yaduwar mugunyar cutar a kasar nan

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel