Coronavirus: Shugaba Buhari ya halarci sallar Juma'a a masallaci

Coronavirus: Shugaba Buhari ya halarci sallar Juma'a a masallaci

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shiga sahun sauran Musulmai da suka gudanar da Sallar Juma'a a masallacin fadar shugaban kasa, Villa, a Abuja.

Sauran ragowar manyan mutanen da suka halarci sallar Juma'a a Masallacin sun hada da babban darektan hukumar leken asiri ta kasa (NIA), Ahmed Rufai Abubakar, da babban darektan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Magaji Bichi.

Jami'an tsaro a Masallacin na yin amfani da wata karamar na'urar gwada dumamar jiki domin gwada masu shiga harabar Masallacin domin yin sallar Juma'a.

Kazalika, jami'an tsaron suna saka ido domin tabbatar da cewa duk wanda ya zo yin Sallah Masallacin ya wanke hannunsa da sinadari na musamman mai kashe kwayoyin cuta da aka ajiye a kofofin shiga harabar Masallacin.

Hakan na faruwa ne a Masallacin duk saboda bullar kwayar cutar coronavirus da duniya ke kokarin dakile yaduwarta.

Coronavirus: Shugaba Buhari ya halarci sallar Juma'a a masallaci
Shugaba Buhari yana Sallah
Asali: Facebook

Bayan tabbatar da bullar kwayar cutar coronavirus, jama'a suna ta kira ga shugaban kasa a kan ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya.

‘Yan Najeriya da yawa sun garzaya shafukansu na sada zumuntar zamani inda suke ta bukatar jin ta bakin shugaban kasa a kan yadda kasar ta shirya tarbar wannan mugunyar cutar da ta addabi fadin duniya.

Amma, ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga ‘yan Najeriya a kan annobar coronavirus bai yi ba.

DUBA WANNAN: Abinda na gani a sansanin 'yan gudun hijira ya firgita ni - Buhari

Mohammed ya sanar da manema labarai cewa Buhari zai yi jawabi ga jama’ar kasar nan a lokacin da ya dace.

Idan lokaci yayi , shugaban kasar zai yi jawabi ,” a cewae Lai Mohammed.

“Amma, a tunanina abinda kuke son ji daga bakin shugaban kasa shine kuke ji daga garemu.

"Ba wai kare shugaban kasar muke ba ko kuma kange shi daga gabatar da jawabi ba, muna da tabbacin cewa zai yi duk abinda ya dace,” kamar yadda Mohammed ya fada bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya a ranar Laraba.

Shugaba Buhari ne ya jagoranci taron na majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da aka yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel