Coronavirus: An dakatad da Khamsu-Salawati a Masallacin Harami da na Annabi (SAW) dake Madina

Coronavirus: An dakatad da Khamsu-Salawati a Masallacin Harami da na Annabi (SAW) dake Madina

Masarautar Saudiyya ta hana shiga Masallatai biyu masu daraja na Makkah da Madina, fari daga ranar Juma'a, 20 ga Maris ga masu khamsu-Salawati cikin matakan da gwamnatin kasar ke dauka wajen takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Kakakin ma'aikatar kula da lamarin Masallacin Harami da Annabi SAW dake Madina ya sanar da hakan ne ranar Juma'a.

A yanzu, mazauna cikin Masallacin da ma'aikata kadai suka sallaci sallar Asuba a yau Juma'a.

Yace: "Hukumomin tsaro da kiwon lafiya sun yanke shawarar hana mutane shiga cikin Masallacin Harami da na Annabi dake Madina fari daga ranar Juma'a 20 ga Maris."

"Hakan yana cikin matakan da kiyaye cigaba da yaduwar cutar Coronavirus."

Ma'aikatar Lafiyan kasar Saudiyya ta tabbatar da cewa kawo ranar Alhamis, mutane 274 sun kamu da cutar.

Sarki Salman bin Abdulaziz a jawabin da ya yiwa al'ummar kasar daren Alhamis ya bayyana cewa gwamnati da daukar dukkan matakan da ya kamata wajen yakar Coronavirus kuma ya bada tabbacin cewa za'a kaiwa ko wani dan kasa magani, abinci, da abubuwa morar rayuwa.

Coronavirus: An dakatad da Khamsu-Salawati a Masallacin Harami da na Annabi (SAW) dake Madina

Coronavirus
Source: Facebook

Kawo yanzu mutane 200,000 sun kamu da cutar a fadin duniya, kuma mutane 10000 sun rigamu gidan gaskiya.

Duk da haka, babu asibitocin gwajin cutar a yankuna hudu cikin shida dake Najeriya.

An tattaro cewa babu asibitocin gwaji a yankun kudu maso gabas, Arewa maso yamma, Arewa maso gabas da kuma Arewa maso tsakiyar kasar.

Hakan ya tayar da hankulan mutane a fadin tarayya saboda tsoron abinda zai biyo baya idan cutar ta bulla a jihohin da ke yankunan nan.

Gaba daya, dakunan bincike biyar ake da shi a fadin tarayya domin gwajin cutar kuma sun yankin Kudu maso yamma da kudu maso kudu.

An tattaro cewa akwai asibitocin gwaji biyu a Legas, daya a jihar Osun, daya a jihar Edo sai kuma guda daya a birnin tarayya Abuja wanda ake sa ran zai kula da dukkan jihohin Arewa.

Majiyoyi sun bayyana cewa ayyuka sun yiwa wadannan asibitoci yawa saboda yan Najeriya dake zuwa domin gwajin kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel