Coronavirus: Duk da matakan da ake dauka, jihohi 4 cikin 36 kadai ke da asibitin kula da cutar

Coronavirus: Duk da matakan da ake dauka, jihohi 4 cikin 36 kadai ke da asibitin kula da cutar

Yayinda cutar Coronavirus ke cigaba da yaduwa a sassan duniya daban-daban musamman a nahiyar Afrika, babu asibitocin gwajin cutar a yankuna hudu cikin shida dake Najeriya.

An tattaro cewa babu asibitocin gwaji a yankun kudu maso gabas, Arewa maso yamma, Arewa maso gabas da kuma Arewa maso tsakiyar kasar.

Hakan ya tayar da hankulan mutane a fadin tarayya saboda tsoron abinda zai biyo baya idan cutar ta bulla a jihohin da ke yankunan nan.

Gaba daya, dakunan bincike biyar ake da shi a fadin tarayya domin gwajin cutar kuma sun yankin Kudu maso yamma da kudu maso kudu.

An tattaro cewa akwai asibitocin gwaji biyu a Legas, daya a jihar Osun, daya a jihar Edo sai kuma guda daya a birnin tarayya Abuja wanda ake sa ran zai kula da dukkan jihohin Arewa.

Majiyoyi sun bayyana cewa ayyuka sun yiwa wadannan asibitoci yawa saboda yan Najeriya dake zuwa domin gwajin kansu.

Coronavirus: Duk da matakan da ake dauka, jihohi 4 cikin 36 kadai ke da asibitin kula da cutar

Coronavirus: Duk da matakan da ake dauka, jihohi 4 cikin 36 kadai ke da asibitin kula da cutar
Source: Twitter

A bangare guda, Hukumomi a asibitin FMC dake Keffi, jihar Nasarawa sun killace mutane biyar yan gida daya da ake zargin sun kamu da cutar Coronavirus da ta addabi kasashen duniya.

Tuni dai an dau jininsu kuma an kai cibiyar takaita yaduwar cuta ta kasa NCDC dake Abuja domin gwaji da tabbatarwa.

Shugaban Asibiti, Dakta Yahaya Baba Adamu, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai ya ce mutane su kwantar da hankulansu.

Dakta Yahaya yace: "Gaskiya akwai yan gida daya a asibitin. Daya daga cikinsu ne ya fara nuna alamu, daga baya sai dukkan yan gidan suka fara nuna alamu irin nasa na zazzabi, mura da sauransu."

"Amma tun da mutmin ya ziyarci jihar Legas da Ogun kwanakin nan. Mun yanke shawarar cewa a mayar da hankali kan lamarin kuma ya kamata a killaceshi."

A cewarsa, mutane hudu cikin biyar da aka killace sun fara samu lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel